Cikin Gwamnoni 18 Ya Duri Ruwa da EFCC Ta Fara Bincike kan Zargin Karkatar da Kudade

Cikin Gwamnoni 18 Ya Duri Ruwa da EFCC Ta Fara Bincike kan Zargin Karkatar da Kudade

  • EFCC ta ce tana gudanar da bincike kan wasu jihohin tarayyar Najeriya bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jama'a
  • Hukumar ta ƙi bayyana cewa binciken na ci gaba da gudana kan yadda ake tafiyar da kudade a wadannan jihohin
  • EFCC ta ce dakatar da amfani da wani asusun gwamnatin Osun mataki ne na doka, ba hari kan wata gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan wasu jihohi.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana gudanar da binciken ne a kusan jihohi 18 bisa zargin almundahanar kuɗaɗen jama'a.

EFCC na bincikar jihohi 18
Shugaban hukumar EFCC na jawabi a wajen taro Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Dalilan EFCC na garkame asusun gwamnatin Osun kafin zabe

Sai dai kakakin na hukumar yaki da cin hanci da rashawar ya ƙi bayyana sunayen jihohin da ake bincike a kansu.

Dalilin EFCC na ƙin bayyana sunayen jihohin

Uwujaren ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayoyi kan matakin da EFCC ta ɗauka na taƙaita amfani da wani asusun gwamnatin jihar Osun.

Ya ce wannan mataki yana daga cikin irin matakan da hukumar ta ɗauka ko kuma take shirin ɗauka kan wasu gwamnatocin jihohi.

Da aka tambaye shi ko akwai wasu jihohin da ake bincike, ya ce:

"Kamar yadda muka bayyana a sanarwar da muka fitar, akwai kusan jihohi 18 da muke gudanar da bincike a kansu."

Da aka matsa masa ya bayyana sunayensu, ya ce:

"Ba na son in fara ambaton sunayen waɗannan jihohi a yanzu."

Lokacin da aka ce ya kamata ya bayyana sunayen domin 'yan Najeriya su sani, Uwujaren ya ce hakan zai iya kawo cikas ga binciken da ake yi.

Kara karanta wannan

EFCC ta rufe asusun gwamnatin jiha sukutum, an jefa gwamna a matsala dab da zabe

"Ba wai muna gudun bayyana sunayen ba ne, amma ba ma son mu kawo cikas ga binciken da ke gudana."

EFCC ta yi karin haske kan matakin jihar Osun

Uwujaren ya ce matakin da aka ɗauka kan jihar Osun ba sabon abu ba ne, domin a baya EFCC ta taƙaita amfani da wani asusun gwamnatin jihar Edo kafin Gwamna Monday Okpebholo ya karɓi mulki.

A cewarsa:

"Kafin zuwan Gwamna Okpebholo, lokacin zaɓen jihar Edo, EFCC ta taƙaita amfani da wani asusun gwamnatin jihar bayan ta gano ana tura kuɗaɗe zuwa wasu asusu masu tayar da shakku."

Ya ƙara da cewa hakan ya taimaka wajen kare kuɗaɗen jihar domin gwamnatin da ta biyo baya ta samu isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukanta.

Uwujaren ya jaddada cewa duk matakan da EFCC ke ɗauka suna bisa tanadin doka, kuma ba a ware wata gwamnati musamman ba.

"Ba mu mayar da hankali kan wata gwamnati ta musamman ba. Abin da muke yi kawai shi ne aiwatar da aikin da doka ta ba mu." In ji shi.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka raba N700m don kifar da gwamnatn Tinubu

Dalilin da EFCC ba ta ɗauki irin wannan mataki a Ekiti ba

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki irin wannan mataki ba lokacin zaɓen jihar Ekiti, Uwujaren ya ce yanayin al'amura ya bambanta. Ya ce hukumar tana da bayanan sirri da ba kowa ne ke da damar saninsu ba.

"Game da abin da ya faru a Ekiti, ba mu da wani dalilin ɗaukar irin wannan mataki. Haka kuma ba ku da damar samun bayanan da muke da su." In ji shi.
EFCC na bincike kan jihohi
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

An kalubalanci shugaban EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kalubalanci shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede.

Gwamna Adeleke ya kalubalanci Olukoyede ya bayyana dalilin da ya sa aka bayar da umarnin rufe asusun gwamnatin jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng