Ma'aikatar Bogi: Yadda Adeniyi Adeyemi Ya Yi Magana da Gbajabiamila

Ma'aikatar Bogi: Yadda Adeniyi Adeyemi Ya Yi Magana da Gbajabiamila

  • Adeniyi Adeyemi mai ikirarin shugabantar PFIPC ya ce bai taɓa haɗuwa da Femi Gbajabiamila ido da ido ba kafin ko bayan ikirarin naɗa shi
  • Ya bayyana cewa duk tattaunawarsa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ta gudana ne ta hannun marigayi Dolapo Tanimola
  • Adeyemi ya sake roƙon shugaban ƙasa ya kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin hukumar PFIPC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar PFIPC, ya bayyana yadda ya yi magana da Femi Gbajabiamila.

Adeniyi ya ce hanyar da ya taɓa yin hulɗa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ita ce ta hannun marigayi abokinsa, Dolapo Tanimola.

Adeniyi ya yi magana kan Gbajabiamila
Shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da Adeniyi Adeyemi Hoto: @femigbaja
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Adeyemi ya bayyana haka ne a ranar Talata, 7 ga watan Yulin 2026 yayin wata hira da Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), yayin da ce-ce-ku-cen da ke tattare da PFIPC ke ci gaba.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Gbajabiamila ya yi barazana kan Adeyemi, zai nemi N10bn

Shin Adeniyi ya hadu da Gbajabiamila?

Ya ce bai taɓa haɗuwa da Gbajabiamila ido da ido ba, ko kafin ko bayan abin da ya kira naɗa shi a matsayin shugaban hukumar PFIPC.

"Ina ganin sau uku na yi magana da Gbajabiamila, kuma hakan ya faru ne ta hannun marigayi abokina, Dolapo Tanimola."

- Adeniyi Adeyemi

Da aka tambaye shi ko ta hanyar kiran bidiyo aka yi tattaunawar, sai ya amsa da cewa:

"A'a, ba ta hanyar kiran bidiyo ba ce."

Fadar shugaban ƙasa ta musanta PFIPC

A watan Yuni, fadar shugaban ƙasa ta nesanta kanta da PFIPC, tana mai cewa babu irin wannan hukuma da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma, Gbajabiamila ya fitar da sanarwa inda ya nesanta kansa da kuma fadar shugaban ƙasa daga Adeyemi, yana mai jaddada cewa ba ofishinsa ko gwamnatin tarayya ba ce ta naɗa shi a kowane matsayi a hukumar da ake ikirarin wanzuwarta.

Kara karanta wannan

Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Adeyemi ya nemi a yi bincike

Da yake magana a hirar, Adeyemi ya ce ba zai iya cewa Gbajabiamila yana ƙarya ba, haka kuma ba zai tabbatar da cewa yana faɗar gaskiya ba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

A cewarsa, bincike mai zaman kansa ne kaɗai zai iya gano hakikanin abin da ya faru.

"Ba zan ce yana ƙarya ba, kuma ba zan ce yana faɗar gaskiya ba. Shi ya sa a taron manema labarai na roƙi mai girma shugaban ƙasa da ya kafa kwamitin bincike domin a binciki wannan lamari gaba ɗaya, a gano gaskiya tare da sanin waɗanda ke da hannu a ciki."

- Adeniyi Adeyemi

Adeyemi ya yi magana da Gbajabiamila
Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Rikicin ya ƙara ɗaukar hankali

Sabbin kalaman Adeyemi sun zo ne kwana guda bayan Gbajabiamila ya yi barazanar shigar da ƙarar neman diyyar naira biliyan 10 saboda zargin ɓata masa suna.

Barazanar ƙarar ta biyo bayan zarge-zargen da Adeyemi ya yi, inda ya danganta Gbajabiamila da cin hanci da kuma mutuwar Dolapo Tanimola.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

A halin yanzu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumar ICPC wa'adin kwanaki 30 domin gudanar da bincike kan wannan takaddama.

Majalisa ta kare kanta kan PFIPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta kare kanta kan badakalar kasafin kudin hukumar PFIPC da ake takaddama a kai.

Majalisar Dattawa ta bayyana cewa ba ta da hannu wajen sanya Naira biliyan 1.3 ga hukumar da ake kira PFIPC, a cikin kasafin kudin shekarar 2026.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa rigimar ta shafi bangaren zartarwa ne musamman tsakanin ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng