Tirkashi: ICPC Ta Cafke Likitan El Rufai, Tsohon Gwamna Ya Aikata Sabon 'Zunubi'

Tirkashi: ICPC Ta Cafke Likitan El Rufai, Tsohon Gwamna Ya Aikata Sabon 'Zunubi'

  • Hukumar ICPC ta zargi tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da karya sharuddan ziyarar asibiti da kotu ta amince masa yayin da yake tsare
  • Hukumar ta kuma kama likitan El-Rufai Farfesa Bello Abubakar bisa zargin bayar da bayanan karya yayin gudanar da binciken da ake yi
  • ICPC, mai binciken cin hanci da rashawa ta ce za ta sanar da kotu yadda aka yi amfani da damar ziyarar asibiti ba bisa manufar umarnin kotun ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar ICPC ta zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da karya sharuddan ziyarar asibiti da kotu ta amince masa yayin da yake tsare a hannunta.

Hukumar ta kuma sanar da kama likitan El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, bisa zargin bayar da bayanan karya, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya hukunci a shari'ar da hukumar EFCC ta nemi ƙwace kadarorin Malami

ICPC ta kama likitan Malam Nasir El-Rufai bayan ta ga hoton tsohon gwamnan da wasu 'yan siyasa.
Farfesa Bello Abubakar (hagu) Isa Ashiru Kudan tare da Malam Nasir El-Rufai. Hoto: @ishaqmasari5
Source: Twitter

Takaddamar El-Rufai da ICPC kan ganin likita

A cikin sanarwar da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar ranar Talata, ICPC ta ce ta amince da ziyarar asibitin ne domin bin umarnin kotu da kuma kare hakkokin wadanda ke tsare a hannunta, in ji rahoton The Punch.

Hukumar ta bayyana cewa Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ware ranakun 6, 7 da 8 ga watan Yulin 2026 domin sauraron karar da ake yi wa El-Rufai cikin gaggawa, amma bai halarci zaman ranar farko ba.

A cewar ICPC, lokacin da jami'anta suka je daukarsa zuwa kotu, ya ki tafiya, yana mai cewa yana son ganin likitansa.

Hukumar ta ce babu wata bukatar ganin likitan da aka gabatar tun kafin wannan lokaci, kuma likitan ICPC ya tabbatar cewa El-Rufai ya ce ba shi da wata matsalar lafiya ta gaggawa.

Zaman jira a shari'ar ICPC da El-Rufai

Sai dai ya bayyana cewa matarsa, Asia El-Rufai, wadda kuma na cikin lauyoyinsa, ita ce ta bukaci ya gana da likitansa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu

Daga baya kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga Yulin 2026 domin yanke hukunci kan bukatar El-Rufai ta sauya alkalin da ke sauraron shari'ar da kuma jiran matakin Babban Alkalin Jihar Kaduna kan bukatar mayar da shari'ar wata kotu.

Hukumar ICPC ta ce duk da dage shari'ar, ta amince da ziyarar asibitin kamar yadda kotu ta umarta.

ICPC ta zargi El-Rufai da keta umarnin kotu

Sai dai hukumar ta ce daga baya ta gano hotunan da wani makusancin El-Rufai a siyasa, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a Facebook, wadanda suka nuna tsohon gwamnan tare da baki da dama ciki har da Farfesa Bello Abubakar a lokacin da aka ware domin duba lafiyarsa.

ICPC ta ce El-Rufai ya keta umarnin kotu
Isa Ashiru Kudan da wasu 'yan NDC sun gana da Nasir El-Rufai a hedikwatar ICPC. Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

A cewar ICPC, hakan ya nuna cewa an yi amfani da damar ziyarar asibitin wajen wasu ayyuka da ba su cikin abin da kotu da hukumar suka amince da shi.

Hukumar ta ce za ta gabatar da wannan batu gaban kotu a matsayin saba umarnin kotu, tana mai jaddada cewa ba za ta amince da cin zarafin kyakkyawar niyyarta ba.

ICPC ta kuma tabbatar da cewa an tsare Farfesa Bello Abubakar domin ci gaba da bincike, tana mai cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa tanadin doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com