Peter Obi Ya Nuna Shakku kan Yiwuwar Takararsa a 2027, "Kila ba Zan Rayu ba"

Peter Obi Ya Nuna Shakku kan Yiwuwar Takararsa a 2027, "Kila ba Zan Rayu ba"

  • Peter Obi ya ce akwai yiwuwar ba zai kai ga tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 ba, inda ya ce wataƙila ba zai kasance a raye ba
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya zargi gwamnatin tarayya da hana shi gudanar da ayyukansa da kuma muzgunawa 'yan adawa
  • Peter Obi ya kuma yi zargin cewa gwamnati ta taso 'yan adawa a gaba inda ya bada labarin wani abu da ya taba faruwa da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya ce akwai yiwuwar ba zai kai ga tsayawa takara ba.

Peter Obi ya bayyana cewa wataƙila ba zai kasance a raye ba domin tsayawa takara a zaben na shekarar 2027 ba.

Peter Obi ya yi magana kan zaben 2027
Peter Obi na jawabi a wajen wani taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya yi a shirin With Chude, wadda fitaccen ɗan jarida, Chude Jideonwo, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Sanata ya zargi Ali Modu Sheriff da ƙoƙarin jefa ƙiyayya tsakanin Obi da ƴan Arewa

Peter Obi ya yi magana kan zaɓen 2027

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ba zai zama ɗan takara a zaɓen 2027 ba, Peter Obi ya bayyana cewa:

"Ba wai kawai ba zan zama ɗan takara ba. Wataƙila ma ba zan kasance a raye ba. Ina gaya muku."
"Duk abin da nake yi a rayuwata, wannan gwamnati tana hana shi gudana. Da gangan suke yi. Komai. Don haka akwai yiwuwar, idan suka samu dama, ba zan kasance a raye ba."

Wace hukuma Obi ya ke zargi?

Sai dai Obi ya bayyana cewa ba ya zargin wata hukuma kai tsaye, amma ya ce yana fuskantar cikas a kusan kowace rana.

"Ba zargi nake yi ba. Na san abin da nake fuskanta. Kullum ina samun tangarda. Abubuwan da ya kamata su zama na yau da kullum ba haka suke ba yanzu.
"Ba za su fito su ce kai tsaye su ne suke yin hakan ba, amma za ka ga alamar su ne a kusan komai."

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku ba zai yi nasara ba a zaben shugaban kasa na 2027'

- Peter Obi

Obi ya ce ana muzgunawa 'yan adawa

Da aka tambaye shi ko shi kaɗai ake kai wa hari, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce abin ya shafi kusan dukkan 'yan adawa.

"Ana kai wa duk wanda yake cikin 'yan adawa hari. Ni ma ana kai mini hari kai tsaye. Komai. Hatta abubuwan da ya kamata a ba ni bisa ƙa'ida ba a ba ni."
Obi ya ba da misalin wani lamari da ya ce ya faru da shi a filin jirgin sama, inda ya yi zargin cewa jami'ai sun kulle motarsa duk da cewa akwai sauran motocin da aka ajiye a wurin.
"Kwanan nan a filin jirgin sama, wasu ma'aikata suka zo suka kulle motata. Na ce musu ni ne. Wanda ke kula da wurin ya ce bai damu ba."
"Na ce ku dubi motocin sauran mutane. Sai na ga suna magana da juna kamar suna tambayar, 'Wane ne wannan?'"

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

- Peter Obi

Peter Obi ya ce ana takurawa 'yan adawa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi bai gabatar da hujja ba

Sai dai Peter Obi bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da waɗannan zarge-zargen ba a lokacin hirar.

Haka kuma, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan ikirarin nasa ba.

Modu Sheriff ya yi zargi kan Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya yi zarge-zarge kan Peter Obi.

Ali Modu Sheriff ya yi zargin cewa Peter Obi yana fafutukar raba Najeriya ne ta hanyar burinsa na zama shugaban kasa.

Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan na Anambra bai taba yin tir da ayyukan haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) ba, ko kuma akidar kungiyar da kudurorinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng