Gobarar Yuni: Yadda Rayuka Suka Salwanta, Mutane Suka Yi Asarar N120m a Kano

Gobarar Yuni: Yadda Rayuka Suka Salwanta, Mutane Suka Yi Asarar N120m a Kano

  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta hallaka mutane biyar tare da lalata dukiyar da ta haura Naira miliyan 120 a Yuni, 2026
  • Hukumar ta samu nasarar ceto dukiyar da darajarta ta kai sama da Naira miliyan 481 tare da gudanar da ayyukan ceto bakwai daban
  • Shugaban hukumar ya bukaci mazauna Kano su yi taka-tsantsan da amfani da wuta domin rage afkuwar gobara da je jawo asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana cewa ta kai daukin gaggawa a lokuta 30 da aka samu tashin gobara a sassan jihar cikin watan Yuni, 2026.

A cewar hukumar, mutane biyar suka rasa rayukansu, yayin da gobarar ta lalata dukiyar da darajarta ta haura Naira miliyan 120.

Kara karanta wannan

An sanya dokar hana fita a Taraba, an kashe dan sanda bayan kisan makiyayi

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta fitar da rahoton ayyukanta a watan Yuni, 2026
Jami'an hukumar kwana kwana suna kokarin kashe wata gobara da ta tashi. Hoto: Stringer/Getty Images
Source: Getty Images

Ayyukan hukumar kashe gobara ta Kano

Sai dai hukumar ta ce ta samu nasarar ceto dukiyar da darajarta ta kai sama da Naira miliyan 481.8 daga gobarar da ta tashi a lokuta daban-daban cikin watan, in ji rahoton Punch.

Bayanan na kunshe ne cikin rahoton ayyukan hukumar na watan Yuni, wanda jami'in hulda da jama'a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa baya ga kashe gobara, hukumar ta gudanar da ayyukan ceto guda bakwai a cikin watan, sannan ta samu kira guda daya da ya kasance na karya.

Haka kuma, an yi nasarar ceto mutane uku daga wasu yanayin gaggawa daban-daban.

Muhimmancin kashe wuta don gujewa gobara

Da yake tsokaci kan rahoton, shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sani Anas, ya bukaci al'ummar jihar su kara yin taka-tsantsan wajen amfani da wuta domin dakile afkuwar gobara da za a iya kauce wa.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca laca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Ya ce ya zama wajibi mutane su tabbatar sun kashe duk wata wuta gaba daya bayan sun gama amfani da ita domin kare rayuka da dukiyoyi.

Anas ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su rika sanya ido sosai kan 'ya'yansu, tare da hana su wasa a kusa da kududdufai, tafkuna, koguna da rijiyoyin da ba a rufe ba.

Hukumar kashe gobara ta ce ta ceto dukiyar fiye da miliyan 400 daga gobara a Kano
Taswirar jihar Kano, inda aka yi gobara har sau 30 a cikin wat 1. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukumar kashe gobara ta ba Kanawa tabbaci

A cewarsa, yin hakan zai taimaka wajen rage yawan hadurran nutsewa cikin ruwa, musamman tsakanin yara da matasa.

Shugaban ya sake jaddada kudurin hukumar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma ta hanyar ba da agajin gaggawa cikin lokaci, wayar da kan jama'a kan matakan kariya da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumar da al'umma.

Ya ce hadin kan jama'a da bin matakan kariya na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage yawan gobara da sauran hadurran gaggawa a jihar.

Gobara ta babbake shaguna a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata mummunar gobara ta kone shaguna kusan 100 a kasuwar kayan hannu da na gida ta Kingsway da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

A yi hattara: Katsina, Sokoto da wasu jihohi 25 za su fuskanci ambaliyar ruwa

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:00 na dare ranar Alhamis kuma ta ci gaba da ci har zuwa safiyar Juma'a.

Hukumar kashe gobara ta Kano ta ce tangardar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, wacce ta jawo asarar daruruwan miliyoyin Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com