Manyan Labarai A Yau
Fargaba ta mamaye Okrika bayan rahoton mutuwar mutane da dama sakamakon shakar hayaƙi mai guba yayin da ake zargin suna ɗibar man fetur ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce jihohi da kananan hukumomi a Najeriya sun amfana matuka sakamakon cire tallafin man fetur a karkashin gwamnatin Tinubu.
An samu labarin rasuwar mai martaba sarkin Gumel a Jigawa Alhaji Muhammad Sani. Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a birnin Cairo na kasar Egypt.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta shirya karrama Lionel Messi ta hanyar dakatar da wasannin gida a minti na 10 domin tafa masa na tsawon minti ɗaya.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi magana kan sauya sunan mashigar Hormuz zuwa “Trump Strait”, kafin daga bisani ya nuna cewa ba da gaske yake nufi ba.
Askarawan Zamfara sun kama mutane tara da ake zargi da taimaka wa ’yan bindiga, ciki har da masu ba da bayanai, masu kai kayayyaki da wani likitan ’yan bindiga.
Tsohon shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Ralph Nwosu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi kuskure wajen cire tallafin man fetur, ya yaba wa shirin Atiku Abubakar.
Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya sake kira da Najeriya ta rungumi tsarin jam'iyyun siyasa biyu domin daidaita fafatawar siyasa da rage rudani.
An sake tona yadda FBI ta kai samame gidan Atiku Abubakar a Maryland a 2005, yayin da ake binciken wani ɗan majalisar Amurka kan zargin cin hanci a Afirka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari