"Ba Boyewa Na Yi ba"; Adeyemi Ya Bayyana Tsoron da Yake Yi kan Badakalar PFIPC

"Ba Boyewa Na Yi ba"; Adeyemi Ya Bayyana Tsoron da Yake Yi kan Badakalar PFIPC

  • Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar PFIPC ya ce dalilin da ya sa ya daina fitowa fili shi ne barazanar da ake yi wa rayuwarsa
  • Ya sake jaddada zargin cewa ya biya Naira miliyan 400 domin samun mukamin shugaban hukumar PFIPC
  • Fadar shugaban kasa ta dage cewa PFIPC ba a san da zamanta ba, yayin da Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) da ake takaddama a kanta, ya yi maganganu.

Adeniyi Adeyemi ya bayyana cewa ba ya boyewa jami'an tsaro, illa dai yana tsoron rasa ransa ne saboda barazanar da yake fuskanta.

Adeyemi na tsoron rayuwarsa
Adeniyi Adeyemi zaune a cikin ofis Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Adeyemi ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2023 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Tv.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Tsoron me yake yi?

Ya bayyana cewa a shirye yake ya bayyana kansa amma yana tsoron halin da rayuwarsa za ta shiga ciki

"A shirye nake na bayyana kaina. Ba na buya. Abin da nake tsoro shi ne rayuwata saboda na samu sahihan bayanai cewa rayuwata na cikin hadari. An yi yunkurin kashe ni sau da dama."

- Adeniyi Adeyemi

Adeyemi ya sake maimaita zargin da ya yi

A yayin hirar, Adeyemi ya ci gaba da ikirarin cewa ya ba shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, kudi domin samun mukamin shugaban PFIPC.

Da aka tambaye shi yadda ya samu Naira miliyan 400 da ya ce an biya ta hannun wani mutum, Adeyemi ya ce aro ya yi.

"Na aro kudin nan, Naira miliyan 400, saboda wannan mukami. Haka ma wadanda na aro kudin wajensu sun kai korafi ga EFCC."

- Adeniyi Adeyemi

Ya bukaci a kafa kwamitin bincike

Kara karanta wannan

PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu

Kalaman nasa sun zo ne sa'o'i bayan ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken lamarin.

​Adeyemi ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya kare kansa idan aka ba shi damar yin hakan ta hanyar da ta dace.

Takaddama kan kasafin kudin 2026

Takaddamar ta kara kamari ne bayan Adeyemi ya yi ikirarin cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya karbi Naira miliyan 400 ta hannun wani wakili, sannan ya nemi karin Naira miliyan 200 domin kammala ba shi mukamin.

Binciken da aka yi a takardar kasafin kudin shekarar 2026 da Ofishin Kasafin Kudi ya wallafa ya nuna akwai wani sashe mai suna "Presidential Economic Advisory Council/Presidential Foreign Intervention Promotion Council", mai lambar 0111062001.

An ware wa wannan sashe jimillar Naira biliyan 1.303, wanda ya kunshi Naira miliyan 802.98 na albashin ma'aikata, Naira miliyan 200 na kashe-kashen gudanarwa da Naira miliyan 300 na ayyukan raya kasa.

Adeyemi ya ce rayuwarsa na cikin hadari
Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar PFIPC Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Fadar shugaban kasa ta musanta sanin PFIPC

Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta musanta cewa akwai irin wannan hukuma, tana mai bayyana PFIPC a matsayin wata hukuma ta kirkira da ba a san da zamanta ba.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Bayan barkewar takaddamar, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan Adeyemi, yayin da Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Adeyemi ya bukaci a bar kotu ta yanke hukunci

Adeyemi ya ce a shirye yake ya kare kansa a gaban kotu, inda ya bayyana cewa:

"Idan ni ne ba daidai ba, kotu ta tabbatar da haka. Idan kuma ni ne ke kan gaskiya, kotu ma ta tabbatar da haka. Abin da ya dace shi ne a yi adalci."

Za a kai Adeyemi gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya, za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban kotu.

'Yan sandan za su gurfanar da Adeyemi wanda yake ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, kan wasu tuhume-tuhume a gaban babbar kotun tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng