Tsugune Ba Ta Kare ba, an Rena Kokarin Tinubu kan Ceto Daruruwan Mutane da Aka Sace

Tsugune Ba Ta Kare ba, an Rena Kokarin Tinubu kan Ceto Daruruwan Mutane da Aka Sace

  • Al’ummar Woro sun bayyana damuwa game da ceto mutane 176 da aka sace bayan shafe watanni shida a hannun yan bindiga
  • Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Kaiama, Yakubu Salihu, ya ce wasu mata masu ciki sun haifi jarirai yayin da suke tsare tsawon watanni shida
  • Sanatocin Arewa sun yaba da jami’an tsaro kan aikin ceto, yayin da al’ummar Woro ta nemi gwamnati ta gaggauta kafa sansanin sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Woro, Kwara - Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Kaiama, Yakubu Salihu, ya bayyana damuwa kan yadda aka sako wasu daga mutane 176.

Sai dai ya ce har yanzu akwai sauran mutane daga cikin wadanda aka sace sabanin rahoton da ake yadawa kan cewa an ceto duka 176 da aka sace.

Har yanzu akwai sauran mutane daga 176 da ba a sako ba a Kwara
Gwamna Abdul Rahman Abdul Razaq na jihar Kwara da Bola Tinubu. Hoto: Kwara state Government.
Source: Facebook

Mutanen da suka rage a hannun yan bindiga

Ya ce mutane 13 har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, bayan ’yan bindiga sun kai hari Woro a ranar 3 ga Fabrairun 2026, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun budewa jama'a wuta

’Yan bindigar sun kai farmaki al’ummar, inda suka kashe sama da mutane 100 tare da yin awon gaba da wasu 176.

A ranar Laraba ne aka ceto mutane 163 daga cikin waɗanda aka sace, lamarin da ya kawo ɗan sauƙi ga iyalansu bayan dogon lokaci.

Salihu ya bayyana cewa wasu mata masu ciki sun haifi jarirai yayin da suke tsare na tsawon watanni shida a hannun masu garkuwa.

Ya ce mutanen da aka ceto, waɗanda yanzu suke jihar Neja, za a mayar da su Kwara kafin ko ranar Asabar domin samun kulawar lafiya.

Ya kuma ce ƙarancin jami’an tsaro da ke yankin ya sa ake samun matsala wajen mayar da martani cikin gaggawa lokacin da aka samu barazana.

Saboda haka, ya ce kafa sansanin sojoji na dindindin zai taimaka wajen ƙara sa ido kan tsaro da kuma rage barazanar hare-haren ’yan bindiga.

An gano sauran mutanen da ke hannun yan bindiga
Taswirar jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi'

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya yi barazana ga Tinubu, zai yi murabus daga jam'iyya mai mulki

Salihu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana ƙoƙarin kafa bataliyar Sojojin Najeriya a yankin domin ƙarfafa tsaro da kare al’umma.

Ya ce al’ummar yankin a shirye take ta samar da wurin da ya dace da kuma dukkan tallafin da ake bukata domin sojoji su fara aiki, cewar Punch.

Har ila yau, ya kuma yaba da amincewar gwamnati da kafa sansanin sojojin, tare da neman a gaggauta kammala shirin domin hana sake faruwar irin wannan hari.

Sanatocin Arewa sun yaba wa Tinubu

A cikin wata sanarwa, sanatocin Arewa sun yaba da jarumta, ƙwarewa da haɗin gwiwar ’yan sanda, DSS, sojoji, NSCDC da ’yan banga.

Sun ce haɗin gwiwar jami’an tsaro da al’umma ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da sakin mutanen da aka sace lafiya.

Sanatocin sun kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda samar da jagorancin siyasa da goyon bayan da ya ƙarfafa jami’an tsaro wajen gudanar da aikin.

Gwamnatin Kwara ta raba wa malamai motoci

An ji cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bai wa Babban Limamin Ilorin da Majalisar Malaman Ilorin motoci hudu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sauko bayan 'yan Katolika sun ja daga, za a tattauna

Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya yabawa gwamnan bisa cika alƙawari da kuma ci gaba da tallafa wa harkokin addini.

Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, ya ce tallafin zai sauƙaƙa zirga-zirgar malaman addini da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.