Gwamnatin Kano Ta Gwangwaje Iyalan Dan Sandan da Ya Rasu a Bakin Aiki
- Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir ta bai wa iyalan marigayi Sufeto Sani Haladu tallafin kuɗi da kayan abinci
- Marigayin dan sandan ya yi bankwana da duniya ne a ranar 27 ga watan Maris, 2026 yayin da yake bakin aikinsa
- Rundunar 'yan sandan Kano ta yabawa gwamnatin jihar kan tallafin da aka bayar ga iyalan mamacin da ya rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta miƙa tallafi ga iyalan marigayi Sufeto Sani Haladu, ɗan sanda da ya rasu yana bakin aiki a ranar 27 ga Maris, 2026.
Tallafin gwamnatin ya ƙunshi gudummawar kuɗi har N1m da kuma kayan abinci da suka haɗa da buhunan shinkafa biyar, buhunan taliya shida, buhunan makaroni shida da kuma jarkoki biyu na man girki mai ɗaukar lita 25 kowanne.

Source: Facebook
Yadda aka miƙa tallafin
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna, ya fitar ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026 a shafin Facebook.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Kano, Mohammed Tajo Othman, ne ya miƙa tallafin a hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar a madadin gwamnatin Kano.
Sanarwar ta ce:
"Tallafin da aka miƙa wa iyalan mamacin ya haɗa da gudummawar kuɗi ta N1m, buhunan shinkafa biyar, buhunan taliya shida, buhunan makaroni shida da kuma jarkoki biyu na man girki mai ɗaukar lita 25 kowanne."
Rundunar 'yan sanda ta yaba
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da sashen ayyuka, Lawal Isa Mani, wanda ya karɓi tallafin a madadin kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Bakori, ya nuna matuƙar godiyar rundunar ga gwamnatin jihar Kano bisa wannan karamci.
Mani ya bayyana marigayi Sufeto Sani Haladu a matsayin jajirtaccen jami'i mai biyayya da kishin ƙasa, wanda ya rasa ransa yayin da yake yi wa ƙasa hidima.

Kara karanta wannan
Umahi: Ma'aikaciyar jinya ta mutu a gida Minustan Tinubu, an zarge shi da boye gaskiya
Ya ce marigayin ya yi wa rundunar da al'ummar jihar Kano hidima cikin ƙwazo da sadaukarwa har zuwa numfashinsa na ƙarshe.

Source: Facebook
Tallafin zai ƙara wa jami'ai ƙwarin gwiwa
Lawal Isa Mani ya ce:
"Matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka abin yabawa ne ƙwarai, kuma yana nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnati da rundunar 'yan sanda."
Ya ƙara da cewa wannan tallafi zai ƙara wa jami'an 'yan sanda masu ci gaba da aiki ƙwarin gwiwa tare da tabbatar musu cewa gwamnati da al'ummar jihar Kano suna ganin sadaukarwar da suke yi kuma suna daraja ta.
Gwamna Abba ya dauki abokin takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki abokin takarar da za su tsaya neman taarce a zaben shekarar 2027.
Gwamna Abba ya yanke shawarar ci gaba da tafiya da mataimakinsa, Murtala Garo, a matsayin abokin takarar sa a zaben gwamna da za a gudanar a shekarar 2027.
A cewar gwamnan, shawarar da ya yanke ta kasance sakamakon sadaukarwa da aminci da Murtala Garo ya nuna tun bayan da ya karbi mukamin mataimakin gwamna
Asali: Legit.ng
