Dalilin da Ya Sa Bala Adamu Ya Amince Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa a 2027
- Bala Adamu Ibrahim ya ce ya amince da zama abokin takarar Gwamna Seyi Makinde na jam'iyyar APM saboda ya yarda da kwarewarsa
- 'Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya bayyana zaben da aka masa a matsayin babban abin alfahari ga Bauchi, Darazo da yankin Sade
- Bala Adamu tsohon ma'aikacin gwamnati ne kuma gogaggen dan siyasa da dan kasuwa, ya taba rike mukaman SSA a gwamnatin Isa Yuguda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APM, Bala Adamu Ibrahim ya bayyana dalilin da ya sa ya amince ya zama abokin takarar Gwamna Seyi Makinde.
Gwamna Makinde na jihar Oyo shi ne dan takarar shugaban kasa na APM a zaben 2027, yayin da daga bisani aka dauko Bala Adamu a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya bayyana yiwuwar haƙura da neman takarar shugaban kasa, ya kawo dalili

Source: Facebook
Daily Trust ta ce da yake tsokaci kan haka, Bala Adamu ya bayyana cewa ya amince da zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ne saboda yana da cikakken yakini cewa Makinde na da kwarewar da za ta ciyar da Najeriya gaba.
Ya ce Bauchi ta samu babban matsayi
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Ibrahim ya ce Makinde ba kawai abokinsa ba ne, har ila yau babban abokin tafiyarsa ne a siyasa.
A cewarsa:
"Ina alfahari matuka da wannan nadin da aka yi min a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APM. Wannan ba kawai girma ne a gare ni ba, har ma wani tarihi ne ga al'ummata da kuma jihar Bauchi."
Bala ya ce tikitin APM ya zama abin alfahari ga jihar Bauchi, karamar hukumar Darazo da kuma al'ummar Sade, domin shi ne karo na farko da dan yankin ya samu irin wannan babban matsayi a siyasar Najeriya.
Wanene Bala Adamu Ibrahim?
Bincike ya nuna cewa Bala Adamu Ibrahim, wanda aka fi sani da Bala Sade, dan siyasa ne kuma dan kasuwa mai shekaru 51. Dan asalin gundumar Sade ce da ke karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.
Shi dan wani tsohon ma'aikacin karamar hukuma ne wanda ya yi aiki a matsayin mai kula da harkokin gandun daji.
Tafiyar Bala Sade a siyasa
Rahotanni sun nuna cewa Bala ya fara aiki a gwamnati tun kafin fara Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999 daga bisani ya yi ritaya.
Bayan haka ya tsunduma siyasa, inda ya nemi kujerar majalisar dokokin jihar Bauchi sau biyu tsakanin 1999 da 2003 karkashin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Darazo.
A zamanin gwamnatin tsohon gwamna Isa Yuguda, an nada shi Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Matasa (SSA), Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Zabe a Hukumar Zaben Bauchi (BOSIEC).

Source: Facebook
Dangantakarsa da Gwamna Makinde
Wata majiya ta kusa da Bala Sade ta bayyana cewa yana da kusanci sosai da Seyi Makinde, har ma ya taba zama daya daga cikin masu taimaka masa.
Majiyar ta ce a wannan lokaci ne dangantakarsu ta kara karfi, lamarin da ya sa Ibrahim ya shafe lokaci mai tsawo yana zaune a Ibadan.
APM ta hango nasarar Makinde
Kun ji cewa APM ta bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takararta na shugaban ƙasa, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, zai yi nasara a zaɓen 2027.
Jam'iyyar ta ce tana ganin Makinde ya samu karɓuwa a wurin 'yan Najeriya a matsayin wanda zai gaji shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
APM ta tabbatar da cewa ta tura sunayen Makinde da sauran 'yan takararta zuwa shafin INEC bayan karbar lambobin shigar da bayanai.
Asali: Legit.ng

