An Yi Aiki Mara Kyau a Majalisa, Akpabio Ya Yi Barazana ga Dan Kwangila

An Yi Aiki Mara Kyau a Majalisa, Akpabio Ya Yi Barazana ga Dan Kwangila

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan ɗan kwangilar da ya gyara ginin Majalisar Tarayya
  • Ya ce matsalolin makirufo (abin magana) da sauran na'urori sun jawo abin kunya ga majalisar da kuma ƙasar Najeriya
  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa shugabancin majalisar na tattara hujjoji kafin ɗaukar matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan ɗan kwangilar da ya gudanar da aikin gyaran ginin Majalisar Tarayya.

Sanata Akpabio ya yi barazanar ne saboda matsalolin kayayyakin sadarwa da suka ci gaba da addabar zauren majalisun biyu.

Akpabio ya yi barazanar ga dan kwangila
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Jaridar Premium ta ce Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026 bayan da sanatoci suka sake fuskantar matsalar rashin aiki yadda ya kamata na makirufo yayin zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kare dangantakar majalisa da Tinubu, ya fadi dalili

An yi kwangila mara kyau a majalisa

Rahoton TheCable ya ce duk da biliyoyin nairorin da aka kashe wajen gyaran ginin Majalisar Tarayya, 'yan majalisa sun ci gaba da fama da matsalolin makirufo, rashin ingancin sauti da kuma na'urar kaɗa ƙuri'a da ba ta aiki tun bayan komawarsu sababbin zauren da aka gyara a watan Afirilun 2024.

Wadannan matsalolin sun sa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka koma amfani da tsarin kaɗa ƙuri'a na hannu yayin tattaunawa kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulki, ciki har da kudirin kafa 'yan sandan jihohi.

Akpabio ya ce za a ɗauki mataki

Akpabio ya ce ya ji kunya matuƙa da halin da kayan aikin suka shiga yayin bikin buɗe taron 'National Assembly Open Week 2026' da aka gudanar a Majalisar Wakilai ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.

"Ya ku masu girma sanatoci, ina fatan kuna lura cewa makirufonmu ba sa aiki yadda ya kamata, domin za mu ɗauki mataki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gwangwaje iyalan dan sandan da ya mutu a bakin aiki

"Na je Majalisar Wakilai jiya domin wakiltarku a wajen buɗe Makon Majalisar Tarayya, kuma ni da Kakakin Majalisar Wakilai mun ji kunya ƙwarai."
"Ɗan kwangilar da ya gyara Majalisar Wakilai shi ne ya yi aikin wannan zauren."
"Idan hakan ya ci gaba, akwai matakan shari'a da za mu iya ɗauka domin tabbatar da an yi aiki mai inganci, domin wannan abin kunya ne ga ƙasarmu."

- Godswill Akpabio

Majalisar na tattara hujjoji

Akpabio ya bayyana cewa shugabancin Majalisar Dattawa na tattara bayanai kan matsalolin kayayyakin da ke ci gaba da faruwa domin amfani da su kafin ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar.

"Ina fatan kuna lura da abin da ke faruwa, saboda idan muka ɗauki mataki kuma suka je kafafen sada zumunta suna korafi, za ku san dalilin da ya sa muka ɗauki wannan mataki. Dukkanmu muna ganin abin da ke faruwa a yanzu,"

- Godswill Akpabio

Akpabio ya yi barazana ga dan kwangila
Sanata Godswill Akpabio a zauren Majalisar Dattawa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Majalisa ta bayar da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar Dattawan ta bayar da tallafi ga wadanda suka rasa rayukansu a kokarin ceto malamai da daliban da aka sace a jihar Oyo.

Majalisar ta ba da tallafin N50m ga iyalan malamai biyu da aka kashe, da kuma iyalan jami’an tsaro uku da suka rasa rayukansu a aikin ceto daliban jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng