Za a Sheka Ruwan Sama na tsawon Kwanaki 3 a Taraba, Kebbi da Wasu Jihohin Arewa

Za a Sheka Ruwan Sama na tsawon Kwanaki 3 a Taraba, Kebbi da Wasu Jihohin Arewa

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa daga Laraba zuwa Juma'a a jihohi da dama, tare da gargaɗin iska mai ƙarfi
  • A hasashen da ta fitar, NiMet ta ce akwai yiwuwar ambaliya a jihohin Imo, Abia, da wasu jihohi uku a cikin wadannan kwanaki ukun
  • Hukumar ta shawarci jama'a su guji tuki lokacin ruwan sama mai ƙarfi tare da bin sababbin rahotannin hasashen yanayi akai-akai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu hadari, tsawa da ruwan sama daga ranar Laraba zuwa Juma'a a sassa daban-daban na ƙasar.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu jihohi, tare da shawartar jama'a su ɗauki matakan kariya domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.

NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama na kwanaki uku a Taraba da wasu jihohin Najeriya.
Ruwan sama da iska mai karfi na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

Jihohin Arewa da za su samu ruwa

Kara karanta wannan

Babban jigon APC a Arewa ya yi magana kan barin jam'iyyar bayan Tinubu ya zabi Shettima

A cikin rahoton hasashen yanayi da ta fitar a Abuja, NiMet ta ce a ranar Laraba za a samu hadari a yankin Arewa, inda ake sa ran tsawa da ɗan ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Taraba da Kebbi, in ji rahoton Vanguard.

Daga bisani kuma, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a jihohin Taraba, Borno, Yobe, Bauchi, Sokoto, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kano da Kaduna.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar ta ce za a samu tsawa da ɗan ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Nasarawa, Neja, Benue da Babban Birnin Tarayya.

Da yamma kuma, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zai mamaye mafi yawan yankin.

An yi gargaɗin yiwuwar ambaliya

NiMet ta yi hasashen cewa jihohin Imo, Abia, Ebonyi, Akwa Ibom da Cross River na iya fuskantar ambaliya a cikin kwanakin hasashen.

Ta ce hakan na buƙatar hukumomin agajin gaggawa a jihohin su kasance cikin shiri domin dakile duk wata matsala da ka iya tasowa.

NiMet ta ba jama'a shawarwari

Hukumar ta shawarci jama'a su killace kayayyakin da iska za ta iya ɗauka domin guje wa haɗurra, kamar yadda rahoton Daily Post ya nuna.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta mutumin da aka kama da laifin ta'addanci

NiMet ta gargadi 'yan Najeriya yayin da ta ce za a samu ruwan sama na kwanaki uku
Wasu yara na wasa yayin da ake ruwa a Nafada, jihar Gombe. Hoto: Jamsy El-nfaty
Source: Facebook

Ta kuma buƙaci mutane su guji tuki yayin ruwan sama mai ƙarfi, su cire na'urorin lantarki daga wutar lantarki lokacin tsawa, sannan su guji fakewa ƙarƙashin manyan bishiyoyi saboda haɗarin faɗuwar rassansu.

NiMet ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama su rika neman rahotannin yanayin filayen jiragen sama daga hukumar domin sauƙaƙa tsara zirga-zirgar jirage.

Haka zalika, ta buƙaci 'yan Najeriya su ci gaba da bibiyar sabbin bayanan hasashen yanayi ta kafafen sadarwar hukumar domin kare rayuka da dukiyoyi yayin daminar bana.

Jihohi 33 za su fuskanci ambaliya

A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatar albarkatun ruwa ta sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya.

Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026.

Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com