Trump Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sauya Manufarsa kan Mashigar Hormuz

Trump Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sauya Manufarsa kan Mashigar Hormuz

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya janye shirin kakaba harajin kashi 20 kan jiragen ruwa masu wucewa ta mashigar Hormuz
  • Ya ce shugabannin ƙasashen Larabawa sun roƙe shi ya maye gurbin harajin da yarjejeniyoyin kasuwanci da zuba jari
  • Sai dai Trump ya ce Amurka za ta ci gaba sanya takunkumi kan jiragen ruwa masu hulɗa da tashoshin jiragen ruwa na Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, D.C, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa ya janye shirin da ya bayyana a baya na kakaba harajin kashi 20 kan jiragen ruwa da ke bi ta mashigar Hormuz.

Trump ya ce maimakon harajin, ƙasashen yankin Gulf za su ƙarfafa zuba jari da kulla yarjejeniyoyin kasuwanci da Amurka.

Shugaba Trump ya fasa karbar haraji kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump a Oval Office Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

A karo na 3 a jere, Amurka ta kai munanan hare hare kan ƙasar musulunci ta Iran

Meyasa Trump ya sauya matsaya?

Shugaba Trump ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa mai amfani da shugabannin ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

"Bayan tattaunawa mai matuƙar amfani da shugabannin Gabas ta Tsakiya, na yanke shawarar maye gurbin harajin kashi 20 da yarjejeniyoyin kasuwanci da zuba jari da ƙasashen Gulf za su yi a Amurka."

- Shugaba Donald Trump

Za a ci gaba da killace tashoshin ruwan Iran

Sai dai Trump ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da aiwatar da abin da ya kira "cikakken killacewa" kan jiragen ruwa masu zuwa ko fita daga tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Ya ce wannan mataki zai fara aiki daga ƙarfe 20:00 agogon GMT na ranar Talata, kuma zai shafi duk wani jirgin ruwa da ke ɗauke da kaya masu alaƙa da Iran.

Rikicin Hormuz ya sake tsananta

Mashigar Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar ɗanyen mai da iskar gas a duniya, ya fuskanci tsaiko bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan

Rashin sani: Shaguben da sanatan Amurka ya yi ga Iran kwana 5 kafin ya mutu

Ko da yake an fara sake buɗe mashigar bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Yuni, rikicin ya sake ɗaukar sabon salo bayan yarjejeniyar ta fara rushewa a makon da ya gabata.

Shugaba Trump ya yi magana kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A ranar Litinin, Trump ya bayyana cewa Amurka ita ce "mai kare mashigar Hormuz", tare da sanar da shirin kakaba manyan kuɗaɗe kan zirga-zirgar jiragen ruwa domin biyan kuɗin tsaron mashigar.

Sai dai wannan sanarwa ta haddasa tashin farashin mai tare da jawo damuwa a tsakanin ƙawayen Amurka, musamman ganin cewa Washington ta taɓa sukar Iran kan shirinta na karɓar kuɗi daga jiragen ruwa masu amfani da mashigar.

Trump ya bar wasiyya kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana abin da yake son a yi wa Iran idan har ta samu nasarar raba shi da duniya.

Trump wanda ya ce Iran ta dade tana farautarsa, ya bayyana cewa ya bayar da umarnin a kaiwa kasar munanan hare-hare idan har aka kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng