Gbajabiamila: Atiku Ya Yi Magana kan Sabuwar Badakalar da Ta Ritsa da Hadimin Tinubu
- Atiku Abubakar ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa Femi Gbajabiamila
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk jami'an gwamnati dole ne su fuskanci bincike ba tare da la'akari da mukaminsu ba
- Femi Gbajabiamila dai bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba, kuma ba a tabbatar da ikirarin ta hanyar bincike mai zaman kansa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci a gudanar da bincike kan sababbin zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Atiku ya jaddada cewa dole ne a dora dukkan jami'an gwamnati kan mizanin daukar alhaki ba tare da la'akari da mukaminsu ba.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran Atiku ya fitar, wadda Paul Ibe ya wallafa a shafin X ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce zarge-zargen sun yi muni matuka da ba za a yi watsi da su ba.
Dalilin yin martanin Atiku Abubakar
Martanin Atiku ya biyo bayan wani rahoto, wanda ya yi zargin cewa Femi Gbajabiamila ya karkatar da kudaden alawus na mai da iskar gas daga hukumar NUPRC bisa wani zargin amincewar shugaban kasa da ake cewa ba ta dace da doka ba.
Rahotanni sun nuna cewa har zuwa yanzu Gbajabiamila bai fito fili ya mayar da martani kan wadannan zarge-zarge ba.
Atiku ya ce batun ya wuce siyasa, domin yana da nasaba da tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnati.
"Wannan batu ya wuce siyasar jam'iyya; yana da alaka da yadda cin hanci da rashawa ke lalata rayuwa da makomar talakawan Najeriya."
Ya zargi gwamnati da nuna bambanci
Atiku ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da ma'auni daban-daban wajen yaki da cin hanci da rashawa.
"Irin wannan cin hanci da rashawa ba a taba ganin irinsa ba, kuma gwamnati ba za ta rika gurfanar da 'yan adawa kan zargin cin hanci ba, alhali cin hanci na kara yaduwa a karkashin idonta."
- Atiku Abubakar
Atiku na so a binciki Gbajabiamila
Ya kara da cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamata ya fuskanci irin matakin da ake dauka kan sauran jami'an gwamnati idan aka yi musu irin wadannan zarge-zarge.
"Ba za ka iya yin wa'azin bin doka ba, alhali jami'anka suna samun kariya daga bincike ba."
"Dole ne a dora Gbajabiamila kan mizani irin na sauran jami'an gwamnati tare da gudanar da bincike mai zaman kansa domin ba shi damar kare kansa daga wadannan zarge-zargen cin hanci da aka yi dalla-dalla a rahoton Gazette."
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Atiku ya tuna da batun Babachir Lawal

Kara karanta wannan
"Shin Rasha ta kashe sanatan Amurka"; An fara nuna yatsa kan mutuwar aminin Trump
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya kuma yi nuni da yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, domin a gudanar da bincike ba tare da katsalandan ba.
"Tsohon shugaban kasa Buhari ya dakatar da Babachir Lawal daga mukaminsa domin a gudanar da bincike cikin 'yanci, don haka bai kamata a ware Gbajabiamila ba."
- Atiku Abubakar
Sakon Atiku ga magoya bayan ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci mambobin jam'iyyar ADC da su kwantar da hankalinsu.
Atiku ya ce Kotun Daukaka Kara ba ta soke zaben fidda gwani da jam'iyyar ADC ta gudanar domin tsayar da 'yan takararta a zaben shekarar 2027 ba.
Asali: Legit.ng

