Turawa Sun Shiga Tashin Hankali, Mutane 10000 Sun Mutu a cikin Kwana 30 kacal

Turawa Sun Shiga Tashin Hankali, Mutane 10000 Sun Mutu a cikin Kwana 30 kacal

  • Kasashen Turai sun samu mutuwar mutane sama da 10,000 fiye da yadda aka saba bayan tsananin zafin rana da ya mamaye yammacin nahiyar a Yuni
  • Fiye da mutum 9,000 daga cikin wadanda suka mutu masu shekaru 65 zuwa sama ne, wadanda suka fi fuskantar barazana daga tsananin zafi
  • Masana sun ce sauyin yanayi da dan Adam ke haddasawa ne ya kara tsananta zafin rana, wanda ya jawo karin mace-mace a kasashe da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasashen Turai sun ba da rahoton mutuwar mutane sama da 10,000, fiye da yadda aka saba a lokacin tsananin zafin rana da ya mamaye yammacin nahiyar a watan Yuni.

Bayanan hukuma sun nuna cewa mafi yawan wadanda suka mutu mutane ne masu shekaru 65 zuwa sama.

Mutuwa na ci gaba da ratsa kasashen Turai yayin da suke fuskantar tsananin zafin rana.
Wata mata tana fifita saboda tsananin zafin rana a Turai. Hoto: SimpleImages via Getty Images
Source: Getty Images

Turai na fuskantar mace-macen mutane

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban makarantar firamare, suna neman N30m kuɗin fansa

Kididdigar da cibiyar EuroMOMO, wacce Hukumar Kula da Cututtuka ta Turai (ECDC) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke tallafawa, ta fitar ta nuna cewa fiye da tsofaffi 9,000 ne suka mutu a wannan lokaci, in ji rahoton Reuters.

EuroMOMO ta bayyana cewa tsananin zafi na iya kashe mutum ta hanyar bugun zafi ko kuma ta kara tsananta cututtukan zuciya da na numfashi, musamman ga tsofaffi.

Babban likita a cibiyar Statens Serum Institut ta Denmark, Lasse Vestergaard, ya ce irin wannan yawan mace-mace a wannan lokaci na shekara ba abu ne da aka saba gani ba.

Ya ce yana da wahala a danganta wannan karin mace-macen da wani abu daban face tsananin zafin rana.

Sauyin yanayi ya kara tsananta a Turai

Masana kimiyya sun bayyana cewa zafin ranan da aka samu a ƙarshen watan Yuni ba zai yiwu ba da ba saboda sauyin yanayi da ayyukan dan Adam ke haddasawa, wanda ke kara yawaita da tsananta irin wannan yanayi.

Bayanan sun tattaro alkaluman mace-mace daga kasashe 27 na Turai tsakanin 22 zuwa 28 ga watan Yuni, lokacin da zafin rana ya fi kamari a Faransa, Spain, Birtaniya da sauran kasashe.

Kara karanta wannan

Bayan saukar Pantami a filin jirgi, gwamnatin Gombe ta yi barazanar bincike

Premium Times ta rahoto cewa masana sun ce babu wata babbar annoba kamar COVID-19 da za ta iya bayyana dalilin karin mace-mace har zuwa 10,650 a cikin wannan mako.

Faransa da Belgium sun fi fama da matsalar

EuroMOMO ta ce ba ta fitar da alkaluman kowace kasa daban ba, amma ta bayyana cewa Faransa da Belgium ne kadai suka samu matakin "mace-mace mai tsanani" a makon karshe na watan Yuni.

Cibiyar lafiya ta Belgium, Sciensano, ta ce wannan shi ne mafi girman adadin mace-mace da aka taba samu a kasar sakamakon zafin rana tun bayan fara tattara irin wadannan bayanai a shekarar 2000.

Rahoto ya nuna cewa dattawa fiye da 9,000 ne suka samu a watan Yunin 2026 a Turai
Wata mata rike da robar ruwa yayin da ake tsananin zafi a Turai. Hoto: fcafotodigital via Getty Images
Source: Getty Images

Wani bincike na daban da Imperial College London da Hukumar Yanayi ta Birtaniya (UK Met Office) da London School of Hygiene and Tropical Medicine suka wallafa ya kiyasta cewa mutane 2,700 sun mutu sakamakon zafin rana a Ingila da Wales kadai a watannin Mayu da Yuni.

Binciken ya nuna cewa kashi 42 cikin 100 na mace-macen sun samo asali ne daga karin zafin da sauyin yanayi ya haddasa.

Zafi na kashe mutane a Turai

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bangar siyasa suka hallaka wani fitaccen malamin Islamiyya a Bauchi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, fiye da mutum 1,300 ne suka mutu a tarayyar Turai tun daga ranar 21 ga Yunin 2026 sakamakon zafi mai tsanani.

Hukumar WHO ta bayyana cewa Turai ce nahiya mafi saurin ɗumama a duniyar yau, inda yanayin zafinta ke ƙaruwa fiye da sauran wurare.

A bayanin da masana suka yi, sun ce sauyin yanayi da dumamar duniya ne ke ƙara yawaita tsananin zafin rana a tarayyar Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com