'Dalilin da Ya Sa Tinubu Zai Samu Gagarumar Nasara a Zaben 2027'
- Karamin Ministan raya yankuna, Alhaji Uba Maigari, ya ce babu wata jam'iyyar adawa ko haɗaka da za ta iya hana Shugaba Bola Tinubu samun nasara a zaɓen 2027
- Ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manufofi da ayyukan raya ƙasa da suka ƙarfafa APC gabanin babban zaɓe mai zuwa
- Maigari ya kuma yi watsi da zargin cewa APC na amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da jam'iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
L- Karamin Ministan raya yankuna, Alhaji Uba Maigari, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Uba Maigari ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin babu wata jam'iyyar adawa ko haɗakar siyasa da za ta iya kawo cikas ga yunkurin Shugaba Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Maigari ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026 yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Mataimakin shugaban APC da wasu manyan ƙusoshi sun fice daga jam'iyyar
Ya ce har yanzu jam'iyyun adawa ba su gabatar da wata madaidaiciyar mafita da za ta iya jawo hankalin 'yan Najeriya su juya wa Shugaba Tinubu baya a zaɓe ba.
"Zan iya tabbatar muku cewa nasarar 2027 za ta kasance babba sosai. Ku dubi 'yan takarar adawa. Bayan yawan sauya jam'iyya, me suka yi da zai sa 'yan Najeriya su zaɓe su? Babu komai," in ji shi.
Maigari ya yabawa gwamnatin Tinubu
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da manufofi da ayyukan raya ƙasa da dama waɗanda, a cewarsa, suka sanya APC cikin kyakkyawan matsayi na samun nasara a babban zaɓe mai zuwa.
Ya lissafa ci gaban ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa ɗan Adam da sauye-sauyen tattalin arziki a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatin.
"Shugaban ƙasa ya aza tubalin samun gagarumar nasara a 2027 ta hanyar aiwatar da muhimman tsare-tsaren ci gaba a fannoni daban-daban na ƙasar nan," in ji Maigari.
Martani kan zargin tsoratar da adawa
Maigari ya kuma yi watsi da zargin cewa APC na amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da jam'iyyun adawa.
A cewarsa, hukumomin gwamnati suna da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu, kuma idan suna bincike ko hulɗa da wasu mutane kan sahihan batutuwa, bai kamata a ɗauki hakan a matsayin tsanantawa ta siyasa ba.
"Hukumomin gwamnati suna da nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su. Idan suna bincike ko mu'amala da wasu kan sahihan batutuwa, bai kamata a fassara hakan kai tsaye a matsayin tsanantawa ta siyasa ba," in ji shi.

Source: Twitter
Tinubu bai so a taba Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima ya ce Tinubu bai taba yarda da daurawa wani laifi ba game da abubuwan da suke faruwa a kasar musamman kan marigayi Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Najeriya.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa abin da ke saurin fusata Shugaba Tinubu shine sukar marigayi Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng
