Kasurgumin Dan Ta'addan ISIS Ya Shigo Najeriya, Sojoji Sun Yi Caraf da Shi

Kasurgumin Dan Ta'addan ISIS Ya Shigo Najeriya, Sojoji Sun Yi Caraf da Shi

  • Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun fatattaki harin ISWAP a Cross Kauwa da ke jihar Borno
  • Sojoji sun kama wani baƙo da ake zargi ɗan ƙasar Morocco ne mai alaƙa da kungiyar 'yan ta'addan ISIS
  • Jami'an tsaro sun ce kamen na iya taimakawa wajen gano hanyoyin kuɗaɗe da alaƙar ƙungiyoyin ta'addanci da ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da mayaƙan kungiyar ISWAP suka kai a Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Bayan fatattakar maharan, jami'an tsaro sun ce binciken da aka ci gaba da yi ya haifar da wani gagarumin nasarar tattara bayanan sirri, inda aka kama wani da ake zargin baƙon ɗan ISIS ne daga wata ƙasar Larabawa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano wasu ƴan ta'addan ƙasashen waje a Borno, sun karya lagon ISWAP

Sojoji sun cafke dan ta'addan ISIS
Dan ta'addan ISIS da sojoji suka cafke a Borno Hoto: @Zagazolamakama
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakaru sun fara sintiri da bincike cikin gaggawa bayan sun tabbatar da tsaron yankin, tare da bin hanyoyin da ake kyautata zaton 'yan ta'addan suka bi yayin da suke tserewa.

Sojoji sun ƙwato kayayyakin ISWAP

A yayin wannan bincike da aka gudanar ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026, dakarun sun sake gano wasu kayan aiki da ake zargin mayaƙan ISWAP sun bari lokacin da suka yi gaggawar janyewa.

Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato akwai manyan na'urorin sadarwa na hannu masu amfani da mitar sadarwa mai ƙarfi da sauran kayan sadarwa da ake ganin suna da muhimmanci wajen bayar da umarni da hulɗar ƙungiyar.

Majiyoyin sun bayyana cewa bayanan sirri da aka samo daga waɗannan kayayyaki ne suka bai wa dakaru damar faɗaɗa bincikensu zuwa yankin tsibiran Tafkin Chadi, har zuwa ƙaramar hukumar Abadam.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

An kama wanda ake zargin ɗan Morocco ne

A cewar majiyoyin sojin, wannan bincike ya kai ga kama wani baƙon da ke ƙoƙarin tserewa, wanda ake zargin Balarabe ne ɗan asalin ƙasar Morocco kuma yana da alaƙa da ƙungiyar ISIS.

Majiyoyin sun ƙara da cewa tuni jami'an leƙen asiri suka fara bibiyar wanda ake zargin bayan binciken ƙwararru da aka gudanar tare da haɗin gwiwar abokan hulɗar ƙasa da ƙasa kan wasu bidiyoyi da aka samo daga kyamarar bidiyo da aka ƙwato bayan artabun Cross Kauwa.

An ce kyamarar ta kasance mallakin wani mai ɗaukar bidiyon ƙungiyar ta'addanci da aka kashe yayin harin da aka dakile.

Sojoji sun cafke dan ta'addan ISIS
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bidiyo ya taimaka wajen gano wanda ake zargi

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kan tura masu ɗaukar bidiyo tare da mayaƙa domin su ɗauki hare-hare don yaɗa farfaganda, ɗaukar sababbin mambobi da kuma tantance yadda hare-haren suka gudana.

Sun ce bidiyon da aka samo daga kyamarar ya ba masu bincike muhimman bayanan da suka taimaka wajen gano wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'in tsaro har da sace mutane a Abuja

Bayan kama shi, an dauki wanda ake zargin cikin gaggawa daga yankin da jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ya kai shi zuwa wani wurin tsaro na musamman, inda ake yi masa tambayoyi da kuma zurfafa binciken bayanan sirri.

Sojoji sun gwabza da 'yan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji biyu da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A yayin harin, an yi rashin sa'a inda mutane uku suka rasa rayukansu sakamakon harbin da ya biyo bayan musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng