Hotunan Jami'a, Gidan Rediyo da Sauran Kadarori 46 da Aka Kwace a hannun Malami

Hotunan Jami'a, Gidan Rediyo da Sauran Kadarori 46 da Aka Kwace a hannun Malami

  • Babbar kotun tarayya ta amince da kwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami
  • Cikin kadarorin da aka kwace akwai jami'ar Rayhaan, gidan rediyon Rayhaan da otal-otal da dama da ke da alaka da tsohon Ministan
  • Kotu ta ce hukumar EFCC ta tabbatar kadarorin ana zargin an mallake su ne da kudaden haramtattun ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta samu nasara a kotu bayan an ba da umarnin kwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

An yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 15 ga Yuli, 2026, bayan kotu ta yanke cewa EFCC ta gabatar da hujjojin da suka isa na nuna ana kyautata zaton an mallaki kadarorin ne da kudaden da ba su fito daga halastattun hanyoyin samun kudin shiga ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Kotu ta kwace kadarori 48 na Malami a Abuja, Kano da wasu jihohi

An kwace kadarorin Malami
Abubakar Malami da daya daga cikin kadarorinsa da aka kwace Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Hukumar EFCC ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026.

Kotu ta tabbatar da kwace kadarorin

Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana cewa masu kalubalantar bukatar EFCC sun kasa gabatar da hujjojin da za su nuna hanyoyin da aka samo kudaden da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin.

Ta ce ba wai ikirarin mallakar kadarori kadai ake bukata ba, dole ne a nuna sahihan hanyoyin samun kudaden da aka saye su da su.

Jami'a da gidan rediyo na cikin kadarorin

Daga cikin kadarorin da aka kwace akwai Jami'ar Rayhaan da ke jihar Kebbi, wacce ta hada da harabarta ta dindindin, ta wucin gadi da kuma haraba ta uku.

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Haka kuma an kwace gidan mataimakin shugaban jami'ar da gidan rediyon Rayhaan da ke kan titin Sani Abacha Bypass a Birnin Kebbi.

Otal-otal da manyan gine-gine

Sauran kadarorin sun hada da manyan otal-otal da gine-gine a Abuja, Kano da Kebbi, ciki har da:

  • Gidan alfarma a unguwar Maitama, Abuja
  • Tsohon Harmonia Hotels da ke Area 11, Garki
  • Meethaq Hotels da ke Jabi mai dakuna 53
  • Meethaq Hotels da ke Maitama mai dakuna 15
  • Gidaje da dama a Asokoro, Gwarimpa, Wuse II da Karsana a Abuja
  • Gidaje da filaye a Kano da Kebbi
  • An kuma kwace shaguna a Wuse Market da Vegas Mall, da wasu kadarori a Apo Legislative Quarters.

Filaye da kadarorin Khadimiyya

Kotu ta kuma ba da umarnin kwace filaye guda biyu masu fadin hekta 100 kowanne da ke kan hanyar Birnin Kebbi zuwa Jega.

Har ila yau, an kwace kadarorin da Khadimiyya for Justice & Development Initiative ta mallaka a Academic Garden City da ke Birnin Kebbi, wadanda suka hada da:

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta canza shawara kan ƙara kuɗin WAEC da NECO a Najeriya

  • Gidaje tara masu dakuna uku
  • Gidaje uku masu dakuna biyu
  • Fili mai fadin hekta 5.4

Masana'antu da cibiyoyin kasuwanci

EFCC ta kwace kadarorin Malami
Wani gida na Malami da kotu ta kwace Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Daga cikin kadarorin da aka kwace akwai:

  • Rayhaan Agro Allied Factory tare da injina, gine-gine, masallaci da gidajen ma'aikata
  • Azbir Arena da ya hada da otal, gidan buga takardu, lambuna, masallaci, Azbir Clothing da Azbir Pharmacy and Supermarket
  • Gidan ajiye tankokin Al-Afiya Energy
  • Rayhaan Security House
  • Wani ginin kasuwanci mai hawa biyu da ba a kammala ba a Birnin Kebbi
  • Ginin gidan mai na Amasdul Oil and Gas Ltd.
  • An kuma kwace kadarorin Zeennoor Hotel da ke Kabuga Satellite Town a Kano mai dakuna 131, da masallacin Zeennoor da tsohon ginin otal din.a

Kalli hotunansu a nan:

Malami ya kare kansa a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya kare kansa a gaban kotu a shari'arsa da EFCC.

Abubakar Malami ya shaidawa kotu cewa kadarorin da EFCC ke neman kwacewa a hannunsa, ya mallake su ne ta hanyoyi halastattu kuma bisa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng