'Yan Bindiga Sun Kai Hari, an Sace Shugaban Makaranta da Dalibai a Kogi
- 'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi yayin da ake gudanar da jarabawar NECO
- Maharan sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu, shugaban makaranta da wani ma'aikacin wucin gadi na NECO
- Rundunar 'yan sanda ta ce an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari makarantar Government Secondary School da ke Odo-Ekina a ƙaramar hukumar Dekina.
Maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026 yayin da ɗalibai ke rubuta jarabawar hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandare ta kasa (NECO).

Source: Original
'Yan bindiga sun sace ɗalibai
Jaridar Tribune ta ce hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026.
Jami'ar hulda da rundunar 'yan sandan ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5:25 na yammacin ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu, shugaban makarantar da kuma wani ma'aikacin wucin gadi na NECO.
An fara aikin ceto mutanen da aka sace
Kakakin rundunar ta ce haɗaɗɗiyar tawagar jami'an tsaro ta fara aikin nema da ceto nan take bayan aukuwar harin, kuma tana ci gaba da bibiyar maharan, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Ta ƙara da cewa an riga an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da cafke waɗanda suka kai harin.
Kwamishinan 'yan sanda zai ziyarci wurin
Sanarwar ta kuma ce Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, CP Naziru Bello Kankarofi, tare da kwamandan Brigade da mai bai wa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin tsaro, suna kan hanyarsu ta zuwa wurin domin tantance halin da ake ciki.
Rundunar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa jami'an tsaro suna ci gaba da aiki domin ceto sauran waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
'Yan sandan sun kuma ce za su fitar da cikakkiyar sanarwa mai ƙarin cikakkun bayanai da aka tabbatar da su yayin da bincike ke ci gaba da gudana.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun sace gawa da masu rakiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu hatsabiban 'yan bindiga sun kai hari kan wata mota da ke dauke da gawar mataimakin kwamandan hukumar kiyayye hadurra ta kasa (FRSC).
Maharan sun sace gawar Augustine O. Ikwue da kuma mutanen da ke rakiyar ta zuwa garinsu na Otukpo da ke jihar Benue a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Majiyoyoyi sun bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan marigayin tare da neman a biya kudin fansa har Naira miliyan 450 domin sakin mutanen da suke tsare da su.
Asali: Legit.ng

