Matsala Ta Tunkaro Trump, 'Yan Majalisa Za Su Yi Masa Bore kan Yaki da Iran
- Jagoran marasa rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka, Chuck Schumer, ya zargi Donald Trump da jefa ƙasar cikin yaƙi da Iran ba tare da amincewar Majalisa ba
- Schumer ya ce jam'iyyar Democrat ba za ta amince da ci gaba da yaƙin da ba shi da izini, tsari ko hanyar kawo ƙarshensa ba
- Ya kuma yi zargin cewa Trump ya yi watsi da dokokin Majalisa tare da kasa bayyana wa Amurkawa manufarsa kan yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Washington, D.C., Amurka - Jagoran marasa rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka, Chuck Schumer, ya soki shugaban ƙasar, Donald Trump.
Chuck Schumer na jam'iyyar Democrat ya soki Shugaba Trump je kan ci gaba da yaƙin Iran ba tare da izinin Majalisar Dokoki ba.

Source: Twitter
Schumer ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.
Chuck Schumer ya ce Trump na ƙara jefa Amurka cikin rikici ba tare da wata cikakkiyar dabara ko hanyar kawo ƙarshen yaƙin ba.
"Donald Trump na ƙara jefa Amurka cikin yaƙi da Iran ba tare da izini ba, ba tare da wani tsari ba, kuma ba tare da hanyar fita daga wannan rikici ba. Jam'iyyar Democrat ba za ta amince da hakan ba."
- Chuck Schumer
Schumer ya ce Majalisa ba za ta yi shiru ba
Sanatan ya ce Trump na sa ran Majalisa za ta yi shiru kan abin da ya kira "yaƙin da ba bisa ƙa'ida ba", duk kuwa da cewa shugaban ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta tare da ƙara tsananta rikicin.
"Sanatocin Democrat sun aika da saƙo a bayyane. Bayan Trump ya sanar da tsawaita wannan yaƙin ba tare da izini ba, ya yi watsi da rinjayen mambobin Majalisa daga jam'iyyu biyu, kuma ya ƙi bayyana wa jama'ar Amurka gaskiya game da kuɗin yaƙin, manufarsa da kuma yadda zai ƙare, ba za mu ci gaba da gudanar da harkoki kamar babu abin da ke faruwa ba."
"Ba za mu ci gaba da harkoki kamar yadda aka saba ba alhali rayukan sojojinmu na cikin haɗari, sannan Trump na haddasa tashin farashin kayan masarufi da man fetur."
- Chuck Schumer
Schumer ya ce Trump ba shi da tsari
Schumer ya dade yana sukar Trump kan yadda yake tafiyar da rikicin Iran. A baya ya bayyana cewa shugaban Amurkan bai san abin da yake yi ba, yana mai cewa yaƙin ya zama babbar masifa.

Source: Getty Images
"Trump bai san abin da yake yi a Iran ba, kuma wannan hanya ce da za ta kai ga mummunan bala'i. Tun daga ranar farko bai da wani tsari ko hanyar kawo ƙarshen wannan yaƙi na ganganci. Yanzu an kai rana ta 136, amma babu abin da ya sauya."
"Rinjayen mambobin Majalisa daga jam'iyyun biyu sun amince da dokar kawo ƙarshen wannan yaƙi, amma Trump ya yi watsi da ita. Sojojinmu na cikin haɗari, yayin da iyalai masu aiki ke biyan kuɗi masu yawa saboda tsadar man fetur da kayan masarufi."
- Chuck Schumer
A ƙarshe, Schumer ya yi kira da cewa:

Kara karanta wannan
"Ku yaki 'yan bindiga"; Tsare tsohon malami ya jawo abin magana ga gwamnatin Katsina
"A kawo ƙarshen wannan yaƙi baki ɗaya."
Trump ya sauya matsaya kan Hormuz
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya soke shirin kakaba haraji kan jiragen da ke wucewa ta mashigar Hormuz.
Shugaba Trump ya bayyana cewa ya soke harajin ne na kaso 20 bayan ya tattauna da shugabannin kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

