Gwamna Kefas Ya Ajiye Mataimakinsa, Ya Zabi Mace a Matsayyin Abokiyar Takara a 2007

Gwamna Kefas Ya Ajiye Mataimakinsa, Ya Zabi Mace a Matsayyin Abokiyar Takara a 2007

  • Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana Hajiya Zainab Abubakar Ibrahim a matsayin wadda zai yi takarar mataimakiyarsa a zaben 2027
  • Sanarwar ta kawo karshen rade-radin siyasa da aka shafe makonni ana yi kan wanda zai zama abokin takararsa
  • An ce matakin zabar Hajiya Zainab zai taimaka wajen karfafa jam'iyyar APC musamman a tsakanin mata da matasa a jihar Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jalingo, Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya zabi abokiyar takara domin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Gwamna Kefas ya sanar da zabar Hajiya Zainab Abubakar Ibrahim, mataimakiyar shugabar mata ta kasa ta jam'iyyar APC, a matsayin mataimakiyarsa a babban zaben 2027.

Kefas ya zabi Hajiya Zainab a matsayin abokiyar takara
Gwamna Agbu Kefas da Hajiya Zainab Abubakar Ibrahim Hoto: Agbu Kefas, Zainab Abubakar Ibrahim
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026 yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a Jalingo.

Kara karanta wannan

Tafiyar Pantami ta samu gagarumar nakasu, tsohon sanata ya yi murabus daga PDP

Sanarwar gwamnan ta kawo karshen makonni na rade-radi da neman goyon baya kan wanda zai kasance tare da shi a tikitin jam'iyyar APC.

Da wannan mataki, Gwamna Kefas ya zama daya daga cikin shugabannin jihohin yankin Arewa maso Gabas na farko da suka zabi mace a matsayin abokiyar takara domin zaben shekarar 2027.

Gwamna ya yabawa Hajiya Zainab

Da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyyar a Jalingo, Gwamna Agbu Kefas ya bayyana Hajiya Zainab Abubakar Ibrahim, wadda kuma take rike da mukamin mataimakiyar shugabar Inter-Party Advisory Council (IPAC) ta kasa, a matsayin muhimmiyar jigo ga jam'iyyar da kuma jihar Taraba.

"Ita mace ce mai biyayya ga jam'iyya, mai hada kan jama'a kuma mai dagewa wajen kare muradun marasa galihu."

- Gwamna Agbu Kefas

Gwamnan ya kara da cewa yakin neman zaben 2027 zai mayar da hankali kan dorewar ci gaba, tsaro da walwala, yana mai cewa gogewar Hajiya Zainab a bangaren mulki da siyasa za ta taimaka wajen cika manufofin gwamnatinsa na ci gaban jihar.

Dalilin zaben Hajiya Zainab

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Majiyoyin siyasa sun bayyana cewa zaben Hajiya Zainab ya kasance cikin dabarun da aka tsara domin tabbatar da daidaito tsakanin yankunan jihar Taraba tare da kara jan hankalin mata da matasa zuwa jam'iyyar.

Wani babban jigon APC a Abuja, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce Hajiya Zainab tana da kwarewar da ake bukata domin samun nasara.

"Tana da kyakkyawar alaka da jama'a a matakin kasa na jam'iyya, tana da gogewa a harkokin siyasa kuma tana da karfin tattara mata a kananan hukumomi 16 na jihar. Gwamnan na bukatar mutum mai tasiri a matakin kasa wanda kuma ya fahimci siyasar Taraba sosai." In ji shi
Hajiya Zainab ta zama abokiyar takarar gwamna Kefas
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, a ofis Hoto: @AgbuKefas
Source: Twitter

Jiga-jigan APC sun bar jam'iyyar

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da suka hada har da mataimakin shugaba, sun fice daga cikinta a jihar Bauchi.

Mataimakin shugaban APC, Ibrahim Misau ya koma PRP ne tare da wasu shugabannin APC na ƙaramar hukuma da na gundumomi a ƙaramar hukumar Misau gabanin zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng