Fadar Shugaban Kasa da Gwamna Makinde Sun Samu Sabani kan Ceto Dalibai a Oyo
- Fadar shugaban kasa ta soki Gwamna Seyi Makinde kan bukatar binciken Majalisar Dinkin Duniya (UN) game da sace dalibai da malamai a Oyo
- Bayo Onanuga ya ce jami'an tsaro sun riga sun yi bayanin yadda aka kubutar da wadanda aka sace, don haka babu bukatar wani bincike na waje
- Ya kuma zargi Makinde da amfani da batun domin cimma muradun siyasa yayin da yake neman takarar shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta caccaki gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kan kiransa da a gudanar da bincike karkashin Majalisar Dinkin Duniya (UN) game da sace dalibai da malamai a jihar.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kiran da gwamnan ya yi na yin bincike, abu ne wanda bai kamata ba.

Source: Facebook
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu
Fadar shugaban kasa ta mayar da martani
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa bukatar gwamnan na nuna rashin amincewa da hukumomin tsaron Najeriya.
A yayin hirar Onanuga ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wata matsala idan Makinde na son UN ta binciki lamarin.
"Gwamnan ya bayyana ra'ayinsa cewa UN ta binciki wannan lamari. Kofofinmu a bude suke. Idan yana ganin akwai wani abu da ya wuce bayanin da sojojinmu suka bayar, to su zo su bincika."
- Bayo Onanuga
Sai dai ya tambayi dalilin wannan bukata, yana mai cewa babu wata hujja da za ta sa jami'an tsaro su jefa 'yan Najeriya, musamman kananan yara, cikin irin wannan wahala da gangan.
Onanuga ya tuna da sadaukarwar jami'an tsaro
Onanuga ya ce aikin ceton ya jawo asarar rayukan wasu jami'an tsaro, ciki har da sojoji da jami'an Amotekun, yayin da suke fafatawa da masu garkuwa da mutanen.
Ya ce ba zai yiwu a yi zargin cewa an shirya a bar yaran su shafe kwanaki 56 cikin wahala ba, musamman ganin cewa wani malamin lissafi ya rasa ransa a lokacin da yake tsare.
"Ku dubi wadannan yara. Wasu ma shekaru hudu ko shida kacal suke da su. Shin akwai wanda zai so da gangan ya jefa su cikin irin wannan azaba na tsawon kwanaki 56?"
- Bayo Onanuga
Fadar shugaban kasa ta zargi Makinde da siyasa
Onanuga ya kuma zargi Makinde, wanda ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa, da sanya siyasa cikin lamarin.
"Abin takaici ne cewa Makinde, watakila saboda siyasa da yake yi a yanzu a matsayin mai neman shugabancin kasa, ba ya amincewa da hukumominmu, sai yake neman wata hukuma daga waje ta zo ta bincika."
- Bayo Onanuga

Source: Twitter
Ya kara da cewa sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun riga sun bayyana duk abin da suka sani game da lamarin, yana mai bayyana bukatar gwamnan a matsayin wadda "ba ta da dalili" kuma "ba ta da wani amfani."
Onanuga ya ce Makinde na kokarin mayar da lamarin tamkar wata muhawarar siyasa.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 da manyan sarakunan Arewa sun cimma matsaya kan kafa yan sandan jihohi
"Mutumin siyasa kawai yake yi, kuma siyasa ce mara kan gado. Yana son amfani da duk wata dama da ya samu, har da kirkiro wata bakuwar ka'idar makirci."
- Bayo Onanuga
'Yan bindiga sun bugi dalibai da malamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabar makarantar da 'yan bindiga suka sace dalibanta a Oyo, ta bayyana bakar wahalar da suka sha.
Shugabar makarantar ta bayyana cewa ita kanta ba a buge ta ba, amma 'yan bindigan sun bugi wasu yaran kanana ba tare da tausaya masu ba.
Asali: Legit.ng
