Manyan Labarai A Yau
Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta bayyana sunayen 'yan takararta na gwamna da mataimakansu a jihohi 28 domin shiga zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa da Najeriya baki daya.
Wata kotun tarayya da ke Amurka ta dakatar da sabon umarnin Shugaba Donald Trump da ke neman takaita damar samun zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa.
Fadar White House ta karyata jita-jitar mutuwar Donald Trump bayan sanarwar wani taron manema labarai da JD Vance zai gudanar ta haifar da ce-ce-ku-ce.
Tsohon dan majalisar wakilai, Ehiozuwa Agbonayinma, ya bukaci Hukumst EFCC ta sake bude bincike tare da gurfanar da Atiku Abubakar kan wasu zarge-zarge.
Gwamna Seyi Makinde ya bukaci a sake duba tsarin kayyade farashin fetur a Najeriya, yana mai cewa a binciki tsarin baki daya ba batun tallafi kadai ba.
Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan rahotannin matasan Najeriya da ake zargin suna sayar da ƙodojinsu domin samun kuɗin rayuwa saboda tsadar rayuwa.
'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun yi kwanton bauna kan ayarin ɗan takarar APC a Borno, Mustapha Gubio, bayan ya dawo daga ziyarar godiya a Damasak
Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta goyi bayan yunƙurin juyin mulkin da ya gaza a Jamhuriyar Nijar, tana mai cewa zargin ƙarya ne kuma bai da tushe.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari