Abu Ya Girma: Maganar Mutuwar Mary Habila Ta Je gaban Majalisar Dinkin Duniya
- Kungiyar Arewa Women Forum for Justice and Good Governance ta kai koke ga hukumar yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNODC) kan mutuwar Mary Habila
- Kungiyar ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaskiya kan yadda Mary Habila ta rasu a gidan David Umahi
- Ta ce irin wannan bincike zai taimaka wajen gano gaskiya tare da kara wa jama'a kwarin gwiwa ga tsarin shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Arewa Women Forum for Justice and Good Governance ta kai koke ga hukumar yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNODC).
Kungiyar tana neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar Mary Habila, kwararriyar ma'aikaciyar lafiya da aka ce ta rasu a gidan Ministan ayyuka, David Umahi, da ke Uburu a jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan
Mary Habila: Dalilin da ya sa iyayen budurwar da ta mutu a gidan Minista ba su so a binciki gawarta

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin takardar koken da aka aike wa wakilin UNODC a Najeriya, wadda shugabar kungiyar, Aisha Bada, ta sanya wa hannu.
Kungiyar ta bukaci hukumar da sauran hukumomin Najeriya da su mara baya ga bincike da ta bayyana a matsayin mai gaskiya, ba tare da son rai ba, kuma cikakke domin gano hakikanin abin da ya faru.
Kungiyar ta bayyana dalilin bukatar bincike
Kungiyar ta ce gudanar da bincike mai zaman kansa ya zama wajibi domin tabbatar da amincewar jama'a da binciken tare da gano gaskiyar abin da ya faru.
A cewar takardar koken, Mary Habila ta mutu ne a yanayin da kungiyar ta bayyana a matsayin abin da ke haifar da tambayoyi, lamarin da ya jawo shakku kan yadda ta kai gidan ministan kafin rasuwarta.
Wani bangare na takardar ya ce:
"Muna rokon UNODC da hukumomin Najeriya da abin ya shafa su goyi bayan gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaskiya kan yanayin da ya haifar da mutuwar Mary Habila."

Kara karanta wannan
Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu
"Bincike mai inganci da ya dogara da hujjojin kimiyyar bincike, shaidun gani da ido da bin doka ne kadai zai iya bayyana gaskiya tare da kara wa jama'a kwarin gwiwa kan tsarin shari'a."
An bukaci a dogara da hujjojin kimiyya
Kungiyar ta yi zargin cewa akwai sabani a bayanan da aka fitar a bainar jama'a game da lamarin, saboda haka ta bukaci masu bincike su dogara da hujjojin kimiyya da bincike wajen gano musabbabin mutuwar.
Har ila yau, ta bukaci a duba wasu zarge-zargen da aka taba yi wa David Umahi a baya, ciki har da zargin cin zarafin mata da sauran batutuwan da ba a warware ba tun lokacin da yake gwamnan jihar Ebonyi.
Takardar ta kara da cewa:
"Ya kamata binciken ya kasance bisa sahihan hujjoji da bin doka kawai. Bayyananniyar gaskiya da daukar matakin da ya dace suna da muhimmanci wajen tabbatar da amincewar jama'a da tsarin shari'a, ba tare da la'akari da matsayin wadanda abin ya shafa ba."

Source: Getty Images
Ba so a binciki gawar Mary Habila
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifin Mary Habila da ta mutu a gidan David Umahi, ya ce ba ya son a binciki gawarta.
A cewar Baba Habila, ya yanke shawarar kada a yi gwajin gawa ne bisa ra'ayinsa cewa babu wani binciken likitanci da zai iya dawo da ran 'yarsa.
Asali: Legit.ng