Abin da 'Yan Sanda Suka Yi Wa Shugaban Ma'aikatar Bogi bayan Cafke Shi

Abin da 'Yan Sanda Suka Yi Wa Shugaban Ma'aikatar Bogi bayan Cafke Shi

  • Jami'an 'yan sanda sun tsare Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaba na hukumar PFIPC
  • An kama shi a jihar Osun kafin aka kai shi Ibadan, daga nan kuma aka wuce da shi zuwa babban birnin tarayya Abuja
  • Ana yi masa tambayoyi kan zargin gudanar da wata hukuma da ake cewa ba ta da sahalewar gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jami'an 'yan sanda sun tsare Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne Darakta Janar na Presidential Intervention Promotion Council (PFIPC).

'Yan sanda na tsare da Adeniyi Adeyemi ne a tsohuwar hedikwatar rundunar Special Anti-Robbery Squad (SARS) da ke babban birnin Abuja.

Yan sanda sun tsare Adeniyi Adeyemi
Adeniyi Adeyemi zaune a cikin ofis Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce an kawo Adeyemi Abuja bayan jami'an Intelligence Response Team (IRT) karkashin jagorancin CSP Moses Lohor sun kama shi, kuma tun daga lokacin ake yi masa jerin tambayoyi.

Kara karanta wannan

Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya

An ruwaito cewa an kama Adeyemi ne a wani wuri da ke jihar Osun kafin aka kai shi Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Daga bisani aka tafi da shi Abuja bayan kotun tarayya da ke Abuja karkashin Mai Shari'a Mohammed Umar ta bayar da sammacin kama shi.

An hango shi yana shiga jirgi

A ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026 an ga Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaba na PFIPC, yana shiga wani jirgin sama mai zaman kansa zuwa Abuja.

Mahukunta sun bayyana PFIPC a matsayin wata hukuma da ke ikirarin ta gwamnatin tarayya alhali ba ta da sahihancin gwamnati.

Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) wa'adin kwanaki 30 domin binciken wannan takaddama tare da mika rahotonta cikin wa'adin.

'Yan sanda sun yi shiru da farko

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda, CSP Anietie Iniedu, domin jin inda Adeyemi yake, ya ce zai bincika sannan ya dawo da bayani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai sake yin karin bayani ba.

Adeniyi Adeyemi na tsare a hannun 'yan sanda
Adeniyi Adeyemi lokacin da 'yan sanda suka cafke shi Hoto: @Yelesowore
Source: Twitter

Wata majiya ta tabbatar da inda ake tsare shi

Sai dai wani babban jami'in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai ya tabbatar cewa ana tsare da Adeyemi a hedikwatar IRT da ke Guzape a Abuja.

Kara karanta wannan

PFIPC: Yadda 'yan sanda suka bankado ma'aikatar bogi a karkashin gwamnatin Tinubu

Majiyar ta ce ana yi wa Adeyemi tambayoyi ne kan zargin gudanar da wata hukuma da ake zargin an gabatar da ita a matsayin hukumar gwamnatin tarayya ba tare da izini ba, tare da wasu ayyuka da hukumomi ke bincike a kai.

"Jami'an IRT ne suka kama shi, ba wasu jami'ai daga wani sashe ba. A halin yanzu yana hedikwatar IRT inda ake yi masa tambayoyi." In ji shi

Gbajabiamila ya kai karar Adeyemi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya maka mai ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi a kotu.

A cikin karar da aka shigar a kotu, Femi Gbajabiamila yana neman a ba shi diyyar Naira biliyan 10 a matsayin diyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng