Peter Obi Ya Jawo Cece Kuce bayan Ya Yi Wasu Kalamai
- Peter Obi ya ce ya ziyarci dukkan makarantun sakandare na jihar Anambra lokacin da yake gwamna, lamarin da ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta
- Wasu sun nuna shakku kan yiwuwar hakan saboda yawan makarantun da ke jihar, yayin da wasu suka kare shi da cewa ya kasance mai yawan ziyartar makarantu
- Ra'ayoyi mabambanta daga magoya baya da masu suka na ci gaba da bayyana kan sahihanci da yiwuwar ikirarin nasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya jawo ce-ce-ku-ce.
Peter Obi ya jawo cece-kucen ne bayan ya ce ya ziyarci dukkan makarantun sakandare da ke jihar a lokacin mulkinsa.

Source: Facebook
The Cable ta ce Peter Obi ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 5 ga watan Agustan 2026 yayin da yake jawabi ga shugabannin Jami'ar Babcock kafin ya gabatar da lakca a taron Babcock International Model United Nations (BIMUN 26) da aka gudanar a Ilishan-Remo, jihar Ogun.
Peter Obi ya yi magana kan ilimi
Obi ya ce ya dace shugabannin siyasa su rika ba bangaren ilimi muhimmanci ta hanyar kai ziyara akai-akai zuwa makarantun firamare, sakandare da jami'o'i domin ganin halin da ake ciki.
Michael Chibuzo ya sanya bidiyon maganar Peter Obi a shafinsa na X.
A cewarsa:
"Jiya ma ina tambayar wani, yaushe ne karo na ƙarshe da shugabanninmu suka ziyarci makarantun firamare, sakandare da jami'o'in da 'ya'yanmu ke karatu? A matsayina na gwamnan Anambra, na ziyarci kowace makarantar sakandare da ke jihar."
Maganar ta jawo muhawara
Bayan wannan furuci, masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara tofa albarkacin bakinsu.
Wasu sun nuna shakku kan yiwuwar ziyarar dukkan makarantun sakandaren jihar, suna mai cewa adadinsu ya yi yawa matuƙa.
Sai dai wasu sun kare tsohon gwamnan, suna cewa ya shahara da kai ziyara zuwa makarantu da ayyukan ilimi a lokacin mulkinsa.
Muhawarar ta ci gaba da ɗaukar hankali, inda magoya bayansa da masu sukar sa ke ci gaba da bayyana mabambantan ra'ayoyi kan sahihanci da yiwuwar ikirarin.
Martanin masu amfani da X
@Adebest001 ya rubuta:
"Ta yaya hakan zai yiwu? Wani ya kamata ya ja hankalinsa kan wasu daga cikin alkawuran da yake yi."
@VincentOjukwu ya rubuta:
"Idan mutum zai iya zagaya yankuna uku ko huɗu na Najeriya tare da yin tafiya zuwa wajen Afirka cikin sa'o'i 24, me zai hana ya ziyarci makarantu sama da 260 cikin shekaru takwas da ya yi a matsayin gwamnan Anambra?"
@Papchilo4224 ya rubuta:
"Duk lokacin da na yi ƙoƙarin yin shiru, sai Peter Obi ya sake yin wani ikirari da yake da wuya a yi watsi da shi. Me ya sa yake yawan yin ikirarin da ake ta muhawara a kai?"
"Ya ce ya ziyarci kowace makarantar sakandare lokacin da yake gwamna. Tun da farko ma ya taɓa cewa ya bai wa kowane shugaban ɗalibai na sakandare a Anambra lambar wayarsa."
"Jihar Anambra tana da sama da makarantun sakandaren gwamnati 260. Yaushe Peter Obi ya samu damar ziyartar dukkansu? Ko dai yana kai ziyara ne da ƙarfe 2:00 na dare?"

Kara karanta wannan
An tono wata doka, Tinubu na iya rasa damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027
@Olaitan_maxy ya rubuta:
"Wannan magana ba ta da gamsasshen tushe. Ba za ka iya ziyartar duka ba. Kuma ba ma wannan ne babban aikin gwamna ba."

Source: Facebook
Peter Obi ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalamansa na baya-bayan nan game da yunwa a Najeriya.
Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NDC ya bayyana cewa kalaman shugaban kasar ba su nuna damuwa da tsananin matsin tattalin arziki da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Asali: Legit.ng

