Shugaban APC Ya Gana da Sanata Hanga yayin da Ake Shirin Raba Shi da Kwankwaso

Shugaban APC Ya Gana da Sanata Hanga yayin da Ake Shirin Raba Shi da Kwankwaso

  • Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufai Sani Hanga a jihar Kano
  • Yilwatda ya ce shugabanni na da alhakin inganta zaman lafiya, ƙarfafa dimokuraɗiyya da fifita muradun al'umma fiye da siyasa
  • Ziyarar na zuwa ne yayin da APC ke ci gaba da ƙoƙarin jawo fitattun 'yan adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufai Sani Hanga, ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan siyasa a jihar Kano.

Legit Hausa ta fahimci cewa ziyarar na zuwa ne bayan tayin da APC ta yi wa Sanatan na ya sauya sheka zuwa cikinta daga jam'iyyar NDC.

Sanata Rufai Hanga ya gana da Nentawe Yilwatda
Farfesa Nentawe Yilwatda tare da Sanata Rufai Hanga Hoto: @nentawe1
Source: Twitter

Farfesa Nentawe Yilwatda ya sanar da kai ziyarar ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben 2027'

Yilwatda ya ce ganawa da Sanata Hanga ta gudana cikin mutunta juna, inda suka fi mayar da hankali kan jin daɗin al'ummar Kano maimakon bambancin jam'iyya.

Yilwatda ya yi kira ga haɗin kai

Da yake magana kan ziyarar, shugaban APC ya ce shugabanni, ko da kuwa suna jam'iyyu mabambanta, suna da nauyin haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

"Ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba, shugabanni suna da alhakin inganta zaman lafiya, ƙarfafa ƙimar dimokuraɗiyya da kuma yin aiki tare domin amfanin al'ummarmu."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Ya ƙara da cewa ci gaban Najeriya zai fi tabbata idan shugabannin siyasa suka gina fahimtar juna, suka ƙarfafa tattaunawa mai amfani, sannan suka fifita jin daɗin 'yan ƙasa sama da muradun jam'iyya.

"Ci gaban Najeriya zai fi tabbata idan muka gina fahimtar juna, muka ƙarfafa tattaunawa mai ma'ana, sannan muka fifita walwalar 'yan ƙasa fiye da siyasar jam'iyya."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Farfesa Nentawe ya ziyarci Rufai Hanga
Sanata Rufai Hanga tare da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @nentawe1
Source: Twitter

Fatan haɗin kan Kano da Najeriya

Farfesa Yilwatda ya bayyana cewa irin wannan ziyara na nuna muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba domin ci gaban jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Abba ya shiga ya fita, APC na shirin raba Kwankwaso da Sanata Hanga

Shugaban na APC ya bayyana fatan cewa irin waɗannan tattaunawa za su taimaka wajen ƙara haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba a Kano da sauran sassan ƙasar.

Sanata Hanga ya yi maganar shiga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Rufai Hanga, ya bayyana cewa ya kasance mai biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya.

Sanata Rufai Hanga ya ce bai yanke shawarar shiga wata jam'iyya ba, duk da kiran da jam'iyyar APC ta yi masa da ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya.

Sai dai, sanatan ya bude kofar sauya sheka inda ya bayyana cewa idan magoya bayansa suka gamsar da shi, zai iya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng