Sanusi II Ya Gano Abin da Ake Bukata don Rage Talauci a Najeriya

Sanusi II Ya Gano Abin da Ake Bukata don Rage Talauci a Najeriya

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce duk wata manufar tattalin arziki da ba ta inganta rayuwar jama'a ba ba ta da tasiri
  • Ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan rage talauci, inganta rayuwa da samar da ci gaban da kowa zai amfana da shi
  • Mai martaba sarkin ya kuma yi kira da a fifita siyasar hidimtawa jama'a, gaskiya da ƙwarewa maimakon siyasar babakere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano – Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan matsalar talauci a Najeriya.

Sanusi II ya bayyana cewa duk wata manufar tattalin arziki da ba ta inganta walwalar al'umma ba, ba za a iya cewa ta yi nasara ba.

Sanusi II ya yi magana kan talauci a Najeriya
Mai martaba Muhammadu Sanusi II a fada Hoto: @MS_Dynasty
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Sarkin ya bayyana haka ne ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026 a Kano yayin wani taro da ƙungiyar PowerShift Africa ta shirya mai taken: "Revisiting the Past, Reconciliation and Building the Future.”

Kara karanta wannan

Umahi: A karshe ministan Tinubu da aka tsinci gawar budurwa a gidansa ya fadi abin da ya faru

Danmadamin Kano kuma Farfesa a fannin tattalin arziki a Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), Abubakar Aliyu Sanusi, ne ya wakilce shi a taron.

Sanusi II ya yi magana kan tattalin arziki

Sarkin ya ce taron ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, zamantakewa da siyasa.

"Ya kamata a rika auna manufofin tattalin arziki ne da irin tasirin da suke yi ga walwalar jama'a. Duk wata manufar tattalin arziki da ba ta inganta rayuwar mutane ba, ba ta da tasiri."

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya buƙaci shugabanni su fifita manufofin da za su rage talauci, inganta rayuwar al'umma da kuma samar da ci gaban da kowa zai amfana da shi.

Ya bukaci a koyi darasi daga tarihi

Sarkin ya jaddada muhimmancin koyon darasi daga tarihi, ƙarfafa cibiyoyi da tabbatar da adalci a matsayin tubalin ci gaban ƙasa.

A cewarsa, babu wata ƙasa da za ta iya gina makoma mai ɗorewa idan ba ta fahimci tarihinta ba kuma ba ta magance matsalolin da suka rage a baya ba.

Kara karanta wannan

Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu

Ya lissafo rashin tsaro, cin hanci da rashawa, talauci da lalacewar ababen more rayuwa a matsayin manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Kira ga shugabanci nagari

Sanusi II ya kuma yi kira da a sauya daga siyasar mamaya zuwa siyasar hidima, gaskiya da ƙwarewa.

"Raba madafun iko bai kamata ya ta'allaka kan tsarin karba-karba a tsakanin yankuna kaɗai ba. Ya kamata a tabbatar da cewa shugabanni nagari, masu ƙwarewa da tausayi ne suke samun damar yi wa al'umma hidima."

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya bayar da shawarwari ga shugabanni
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II Hoto: Sanusi Dynasty
Source: Twitter

Sarkin ya buƙaci 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da bambancin addini ko siyasa ba, su rungumi haɗin kai, haƙuri da ɗaukar nauyin gina ƙasa tare.

Ya ƙara da cewa ƙasar na cikin wani muhimmin mataki da ke buƙatar yin nazari na gaskiya kan abin da ya faru a baya domin gina makoma mai kyau.

Tinubu ya kaddamar da shirin rage talauci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da gagarumin shirin tallafi da ci gaban al'umma guda biyar na dala biliyan 3.05 domin yaƙi da talauci a Najeriya.

Shugaban kasar ya bayyana shirye-shiryen a matsayin wani babban mataki na gaggawa da zai rage talauci, ƙarfafa al'umma, da kuma haɓaka bil'adama a faɗin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng