'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto, an Sace 'Yan Gudun Hijira

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto, an Sace 'Yan Gudun Hijira

  • Wasu mutane da suka dawo gidajensu daga gudun hijira sun fada hannun 'yan bindiga bayan sun kawo hare-hare a karamar hukumar Tambuwal
  • Maharan sun yi awon gaba da mutane tare da kwashe dabbobi bayan sabon harin da suka kai a jihar Sokoto
  • Iyalan da suka rasa matsuguni sun bukaci gwamnati ta kai musu ɗauki cikin gaggawa domin farfadowa daga asarar da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Wasu daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga, kuma suka koma garuruwansu, sun fada hannun mahara a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kai wani sabon hari a kauyuka guda biyu na Tungar Barke da Gasalodi a ƙaramar hukumar Tambuwal.

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2026 da misalin ƙarfe 11:00 na safiya.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara taso Najeriya a gaba game da kare rayukan kiristoci

'Yan bindiga sun sace 'yan gudun hijira

An dai kai harin ne yayin da mazauna yankin, waɗanda suka shafe lokaci suna neman mafaka a garin Jabo bayan hare-haren da suka gabata, suka fara komawa gidajensu.

'Yan bindigan sun kuma sace dabbobi masu yawa da ba a san adadinsu ba kafin su tafi da mutanen da suka yi garkuwa da su.

Wani mazaunin Jabo ya tabbatar da cewa mutanen da abin ya shafa sun koma garuruwansu ne kwana ɗaya kacal kafin sabon harin.

An sace dabbobi da dama

Ya ƙara da cewa tun da farko maharan sun yi wa mazauna ƙauyukan barazanar cewa za su dawo idan suka sake komawa gidajensu.

"Sun faɗa musu cewa da zarar sun koma, za su dawo. Hakan kuwa shi ne ya faru." In ji shi

Wani mazaunin yankin ya kiyasta cewa kimanin mutane 20 ne aka sace a harin.

"Ina gona lokacin da na ga mutane suna gudu suna komawa Jabo domin tsira da rayukansu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Jama'a sun sake tserewa

Ziyarar da aka kai garin Jabo ta nuna cewa mutane da dama da suka sake rasa matsugunansu suna samun mafaka a makarantun gwamnati, yayin da wasu kuma suka taru a gefen manyan hanyoyi bayan tserewa daga sabon harin.

Daya daga cikin matan da suka rasa matsuguni, Yarmagaji, bazawara ce mai 'ya'ya biyar daga kaiyen Tungar Barke. Ta ce ta shafe fiye da wata guda tana zaune a makaranta bayan da aka raba ta da gidanta.

'Yan bindiga sun sace mutane a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook
"Ina da yara biyar marayu. Tun da muka zo nan kusan wata guda da ya wuce, bara nake yi domin ciyar da su saboda ba ni da wata hanyar samun abin rayuwa." In ji ta

Ta roƙi ƙaramar hukumar Tambuwal da sauran hukumomin da abin ya shafa su kai kayan tallafi ga iyalan da suka rasa matsugunansu.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa'i, ya ce har zuwa lokacin bai samu cikakken bayani kan harin ba, amma ya yi alƙawarin bayar da ƙarin bayani da zarar an sanar da shi.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jiragen sojoji sun far wa taron 'yan bindiga 300 a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wata makarantar sakandare a jihar Kogi.

Hatsabiban 'yan bindigan sun sace dalibai, shugaban makaranta da wani ma'aikacin hukumar shirya jarabawa ta NECO.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng