Ana Murna da Gwamna Mutfwang Ya Mayar da Babban Basarake kan Kujerarsa
- Al'ummar masarautar Bashar sun yabawa Gwamna Caleb Mutfwang kan mayar da Alhaji Abdullahi Idris kan kujerarsa ta Rekna na Bashar
- An dakatar da basaraken ne tun ranar 2 ga Oktoba, 2024, kafin daga bisani Gwamna Mutfwang ya dawo da shi kan sarauta
- Kungiyar BACCODA ta ce matakin zai ƙara ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a Bashar da jihar Plateau baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jos - Al'ummar Masarautar Bashar da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Plateau sun yabawa Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang bisa mayar da Mai Martaba Alhaji Abdullahi Idris kan kujerarsa ta Rekna na Bashar, wanda shi ne babban basaraken yankin.
Gwamna Mutfwang ya dakatar da basaraken ne a ranar 2 ga Oktoba, 2024, amma gwamnan ya mayar da shi kan sarauta a kwanakin nan.

Source: Facebook
Wata majiya daga Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta ta jihar Plateau ta tabbatar da batun mayar da shi ga jaridar Daily Trust a Jos.
BACCODA ta yabawa Gwamna Mutfwang
Ƙungiyar Bashar Chiefdom Community Development Association (BACCODA) ta bayyana matakin a matsayin babban nasara ga al'ummar Bashar da ma jihar Plateau baki ɗaya.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Dakta Zakari Mohammed, da sakatarenta, Alhaji Yunusa Aliyu Garba, suka sanya wa hannu a ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026.
Kungiyar BACCODA ta ce matakin gwamnan ya nuna nagartaccen shugabanci, dattako da kuma ƙudurin tabbatar da haɗin kai a matakin al'umma, kare al'adu da inganta zaman lafiya a faɗin jihar Plateau.
Sanarwar ta ce:
"Mu a BACCODA, a madadin daukacin al'ummar Masarautar Bashar, muna miƙa godiya da yabo ga Mai Girma Gwamna Caleb Mutfwang saboda wannan mataki mai cike da adalci da haɗin kai."
"Mayar da Rekna na Bashar kan kujerarsa nasara ce ga adalci, gaskiya da kuma burin al'ummarmu na ci gaba da kare martabar cibiyoyin gargajiyarmu. Wannan ya nuna gwamnan yana sauraron muradun jama'a tare da fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen siyasa."

Source: Original
An ce matakin zai ƙara zaman lafiya
BACCODA ta bayyana cewa warware rikicin masarautar Bashar zai ƙara ƙarfafa ƙoƙarin gina zaman lafiya a mazaɓar tarayya ta Wase da kuma jihar Plateau baki ɗaya.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga al'ummar Masarautar Bashar da daukacin mazauna ƙaramar hukumar Wase da su mara wa sarakunansu baya, su kiyaye doka da oda, tare da ci gaba da goyon bayan ayyukan ci gaban da gwamnatin jihar Plateau ke aiwatarwa.
A ƙarshe, BACCODA ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗa kai da gwamnatin jihar, masu ruwa da tsaki a harkokin gargajiya, da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin samar wa al'ummar Wase ƙarin ribar dimokuraɗiyya da ci gaba mai ɗorewa.
'Yan bindiga sun kashe basarake a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kashe Dagacin Gwande da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos a Jihar Plateau, Saf Samuel Alaket.
'Yan bindigan sun kashe basaraken ne a wani harin kwanton bauna da aka kai masa a kan hanyar mazaɓar Sha da ke iyaka da garin Daffo.
Asali: Legit.ng

