Kotun Daukaka Kara Ta Jikawa INEC Aiki, Ta Soke Wasu Sassan Dokar Zabe ta 2026
- Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta soke wasu sassan Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi zaben fidda gwani da rajistar mambobin jam'iyyun siyasa
- Kotun ta ce sassan dokar sun ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya saboda sun takaita ikon jam'iyyu kan harkokinsu na cikin gida
- Alkalan kotun sun bayyana cewa hukuncin ya shafi wasu ƙananan sassa ne kawai, ba duka sashe na 77 da na 84 na dokar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta soke wasu muhimman sassan Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi zaben fidda gwani na jam'iyyun siyasa da kuma rajistar mambobinsu.
Sassan dokar da abin ya shafa su ne sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da kuma sashe na 84(2) na Dokar Zabe ta 2026 da aka yi wa kwaskwarima, wadda Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a watan Fabrairun 2026.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ce hukuncin kotun na ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026 ya zo ne watanni shida kacal kafin gudanar da babban zaben shekarar 2027.
Dalilin da kotu ta yanke hukuncin
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari'a Balkisu Aliyu ya yanke hukuncin a ranar Alhamis.
Kotun ta bayyana cewa sassan dokar da aka kalubalanta sun ci karo da sashe na 221 da na 222 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
A cewar kotun, kundin tsarin mulkin ya bai wa jam'iyyun siyasa ikon yanke shawarar wadanda za su tsayar takara a zabubbuka, don haka dokar ba za ta iya tauye wannan iko ba.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan karar da jam'iyyar Zenith Party ta shigar mai lamba CA/ABJ/CV/750/2026. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce ke matsayin wadda ake kara a shari'ar.
Abin da Kotun Daukaka Kara ta bayyana

Kara karanta wannan
Ana shirin zaben 2027, an ruguza lissafin APC a Amurka, Birtaniya da wasu kasashen waje
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa mai shari'a Eberechi Nyesom-Wike, wadda ta karanta babban hukuncin kwamitin alkalan, ta soke sashe na 77(6) saboda ya bai wa INEC iko mai yawa kan harkokin cikin gida na jam'iyyun siyasa.
Kotun ta kuma soke sashe na 77(7) saboda yana iya hana jam'iyyun siyasa amfani da hakkinsu na kundin tsarin mulki wajen tsayar da 'yan takara.
Wannan sashe ya tanadi cewa jam'iyyar siyasa ba za ta shiga zabe ba idan ta kasa mika rajistar mambobinta ga INEC cikin wa'adin da aka kayyade.
Sai dai kotun ta ce wannan tanadi zai yi katsalandan ga ikon jam'iyyun siyasa na gudanar da tsarin tsayar da 'yan takararsu yadda ya kamata.
Hakazalika, kotun ta ayyana sashe na 84(2) a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki, inda ta soke shi saboda ya takaita jam'iyyun siyasa ga amfani da zaben fidda gwani kai tsaye ko tsarin maslaha kawai wajen tsayar da 'yan takara.
Kotun ta ce wannan tanadi katsalandan ne da majalisa ta yi cikin harkokin cikin gida na jam'iyyun siyasa.

Source: Facebook
Kotu ta yi karin haske
Mai Shari'a Nyesom-Wike ta bayyana cewa hukuncin ya shafi ƙananan sassan sashe na 77 da na 84 da aka ambata ne kawai, ba dukkan sassan dokar ba.
Ta kara da cewa tanadin da ya wajabta wa jam'iyyun siyasa mika rajistar mambobinsu ga INEC yana nan daram.
Abin da aka soke shi ne tanadin da ya kayyade takamaiman wa'adin da dole a mika rajistar mambobin ga hukumar zaben.
INEC za ta yi zaben gwaji
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar INEC na duba yiwuwar gudanar da cikakken bincike a kan na'urorinta da shirya zaben gwaji domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar INEC ta bayyana cewa tana da niyyar magance duk wani kuskure ko giɓi da aka gano a zaɓukan baya kafin shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

