Gwamna Nasir Ya Waiwayi 'Yan NYSC, Za a Fara Biyansu Alawus a Kebbi
- Gwamnatin Kebbi za ta fara biyan masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) alawus na Naira 10,000 duk wata
- Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki
- Ya buƙaci masu bautar ƙasar su kasance masu ƙwazo, ladabi da jajircewa wajen gudanar da aikinsu a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Kebbi, jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta fara biyan masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) alawus.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa za a fara biyan masu yin NYSC da ke aiki a jihar Kebbi alawus na Naira 10,000 duk wata.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron bita na shugabannin NYSC da masu ɗaukar masu yi wa ƙasa hidima aiki na shekarar 2026 da aka gudanar a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya zakulo samari da zawarawa 300, zai masu auren gata da sadakin N250000 a Kebbi
Masu NYSC za su samu alawus a Kebbi
Taron ya gudana ne ƙarƙashin taken, "Ƙarfafa haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki domin inganta jin daɗi da ƙwarewar aiki na masu bautar ƙasa."
Gwamnan, wanda kwamishinan wasanni da ci gaban matasa, Alhaji Nurudeen Bala-Fingilla, ya wakilta, ya ce duk masu bautar ƙasa da ke yi wa jihar Kebbi hidima za su amfana da wannan alawus.
Alhaji Bala-Fingilla, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanarwar NYSC a jihar, ya ce an ƙaddamar da wannan shiri ne domin rage wa matasa radadin hauhawar farashin kayayyaki.
Ya ƙara da cewa jihar Kebbi na ci gaba da kasancewa tamkar gida na biyu ga masu bautar ƙasa da ke gudanar da hidima a jihar.
Gwamna ya yi kira ga masu bautar ƙasa
Gwamna Idris ya buƙaci waɗanda za su ci gajiyar wannan tallafi su mayar da biki ta hanyar nuna ƙwazo, ladabi, jajircewa da sadaukar da kai a wuraren da aka tura su aiki domin amfanin al'ummomin da suke yi wa hidima.
Har ila yau, ya jaddada cewa ya rataya a wuyan duk masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa masu bautar ƙasa ba wai kawai suna gudanar da aiki mai amfani ba ne, har ma suna aiki a yanayi mai kyau, aminci da cikakken goyon baya a tsawon shekarar hidimarsu.

Source: Original
NYSC ta yi kira ga masu ɗaukar aiki
A nasa jawabin, babban daraktan NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, wanda daraktar riƙo ta ofishin shiyyar Arewa maso Yamma, Eghieye Mary, ta wakilta, ya ce wurin aiki shi ne babbar dama da masu bautar ƙasa ke samun ƙwarewa ta zahiri.
Ya buƙaci masu ɗaukar masu bautar ƙasa aiki su ba su ayyukan da suka dace da iliminsu da ƙwarewarsu, tare da samar musu da jagoranci, kulawa da damar bunƙasa sana'arsu.
Nafiu ya ce hukumar NYSC na yabawa waɗanda ke samar wa masu bautar ƙasa masauki, tallafin sufuri, kula da lafiya, jagoranci da sauran nau'o'in tallafi.
Dalilin Tinubu na yin gyara a NYSC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta amince da gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima na NYSC.
Shugaba Tinubu ya ce gyare-gyaren na da nufin wadatar da matasan Najeriya da fasahohin aikace-aikace da kuma shirya su domin ci gaban kasa.
Asali: Legit.ng
