Shugaban EFCC Ya Shiga Tsaka Mai Wuya kan Rufe Asusun Gwamnati da Umarnin Tinubu

Shugaban EFCC Ya Shiga Tsaka Mai Wuya kan Rufe Asusun Gwamnati da Umarnin Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya umurci EFCC ta janye matakin rufe asusun gwamnatin Osun lamarin da ya jawo maganganu
  • Gwamnatin Osun ta kai EFCC kotu, tana neman a soke daskarar asusun tare da biyan N2bn diyya saboda saba doka
  • Atiku Abubakar da ADC sun soki matakin, yayin da kungiyoyin fararen hula da lauyoyi suka ce ya kamata a bi doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na umartar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta janye rufe asusun gwamnatin Osun ya haifar da sabuwar cece-kuce.

Jam’iyyun adawa sun fara tambayar dalilin bayanin shugaban, yayin da lauyoyi da kungiyoyin fararen hula suka goyi bayan matakin Tinubu na hana abin ya shafi zaben jihar.

Umarnin Tinubu ga EFCC kan rufe asusun gwamnati
Gwamna Adeleke Ademola da Shugab Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gwamnatin Osun ta garzaya kotu

Kara karanta wannan

'Babu kamar shi': An fadi bangaren da Tinubu ya fi sauran shugabannin Najeriya

Gwamnatin Osun kuwa ta garzaya kotu, yayin da dimbin ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta suka bukaci a yi murabus ko a cire shugaban EFCC, Ola Olukoyede, cewar Punch.

A ranar Laraba, EFCC ta umurci cewa kada a cire wani kudi daga asusun rabon kudaden tarayya na gwamnatin Osun.

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan gano wasu mu’amalolin kudi da take zargi da rashin gaskiya, yayin da take gudanar da bincike kan N11bn.

Gwamnatin Osun ta kai EFCC kotu

Gwamnatin Osun ta shigar da kara a kan EFCC a ranar Alhamis, tana neman kotu ta soke matakin daskarar da asusun jihar.

Ta kuma bukaci kotu ta umurci EFCC ta biya N2bn a matsayin diyya mai tsanani saboda abin da ta bayyana a matsayin cin zarafin ikonta.

Gwamna Ademola Adeleke, Antoni-Janar na jihar da Akanta-Janar na jihar ne suka kasance masu shigar da kara a gaban kotun.

A bangaren wadanda ake kara kuwa, akwai EFCC, shugabanta Ola Olukoyede da bankin First Bank.

Gwamnatin ta bukaci kotu ta tantance ko umarnin EFCC ga bankin na daskarar da asusun bai saba wa dokokin kasa da kundin tsarin mulki ba.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin marigayi Buhari ta kashe N1.16trn na tallafin man fetur

ADC ta soki Tinubu

Jam’iyyar ADC, ta yi maraba da matakin Tinubu na janye daskarar asusun, amma ta ce bayanin shugaban ya kara haifar da tambayoyi.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya kalubalanci Tinubu da ya bayyana dalilin da ya sa yake ta ambaton wani umarnin kotu.

Jam’iyyar ta ce EFCC ba ta taba bayyana cewa ta samu umarnin kotu kafin daskarar asusun ba a cikin bayanan da ta fitar, cewar Vanguard.

An taso shugaban EFCC ya yi murabus
Shugaba Bola Tinubu da shugaban EFCC, Ola Olukoyede. Hoto: EFCC, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Atiku ya soki matakin Tinubu

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce matakin Tinubu ya nuna cewa shugaban kasa na da iko kan ayyukan hukumomin yaki da cin hanci.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce Tinubu ba zai iya ci gaba da cewa EFCC na aiki ba tare da tasirin fadar shugaban kasa ba.

Atiku ya ce daskarar da babban asusun gwamnatin jiha a gabanin zaben gwamna na iya kawo cikas ga gudanar da gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maka EFCC a kotu bayan rufe asusun gwamnatinsa ana shirin zaɓe

Ana matsa wa shugaban EFCC

Rikicin ya kuma jawo suka mai yawa ga shugaban EFCC, Ola Olukoyede, musamman a kafafen sada zumunta kamar X da Facebook.

Wasu masu amfani da X sun bukaci Olukoyede ya yi murabus, suna zargin cewa ci gaba da kasancewarsa a matsayin shugaban EFCC na rage martabar hukumar.

Tinubu ya fusata kan rufe asusun gwamnatin Osun

An ji cewa Bola Tinubu ya fitar da sanarwar da ya sanya wa hannu da kansa, inda ya umarci EFCC ta koma kotu domin soke umarnin daskarar da asusun.

Shugaban ya ce duk da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba, lokacin da aka dauki matakin bai dace ba

Tinubu ya ce ya ji matukar kunya ba saboda EFCC ta gudanar da aikinta bisa umarnin kotu ba, sai dai saboda lokacin da hukumar ta zabi daukar matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.