"Zan Yi Murabus daga Ministan Abuja"; Wike Ya Kafa Sharadin Barin Ofis

"Zan Yi Murabus daga Ministan Abuja"; Wike Ya Kafa Sharadin Barin Ofis

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci duk mai musanta nasarorin gwamnatinsa kan titunan ƙauyukan birnin tarayya ya fito cikin sa'o'i 48
  • Wike ya ce gwamnatin Abuja ta ba da kwangilar kilomita 317 na tituna, ta kammala kilomita 221, yayin da ake ci gaba da aikin kilomita 96
  • Ministan na Abuja ya bayyana cewa zai yi murabus idan aka tabbatar da cewa bayanan da ya bayar ba gaskiya ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya ƙalubalanci duk wanda ke musanta irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi na gina tituna a ƙauyukan Babban Birnin Tarayya da ya fito fili ya karyata shi cikin sa'o'i 48.

Wike ya ce idan aka tabbatar da cewa bayanan da ya gabatar ba gaskiya ba ne, zai yi murabus daga mukaminsa na ministan Abuja.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Wike ya yi alkawarin yin murabus
Ministan Abuja, Nyesom Wike na jawabi ga manema labarai Hoto: @Olayinkalere
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 17 ga watan Yulin 2026 yayin ƙaddamar da aikin sake gina titin Arab/Gbazango da ke Kubwa.

Ministan ya yi bayani kan nasarorin da gwamnatin Babban Birnin Tarayya ta samu ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kilomita 317 na tituna aka ba kwangila

A cewar Wike, tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin Abuja ta ba da kwangilar gina kilomita 317 na tituna a ƙauyukan Babban Birnin Tarayya.

Ya ce daga cikin wannan adadi, an kammala aikin kilomita 221, yayin da ake ci gaba da aikin sauran kilomita 96.

"Yayin da nake magana da ku yanzu, tun bayan hawan shugaban ƙasa mulki, an ba da kwangilar kilomita 317 na tituna a ƙauyukan Babban Birnin Tarayya. Daga ciki, an kammala kilomita 221, yayin da ake ci gaba da aikin kilomita 96."

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gano abin da ake bukata don rage talauci a Najeriya

- Nyesom Wike

Ministan ya jaddada cewa waɗannan alkaluma sun shafi ƙauyukan Abuja ne kawai, ba tare da haɗa sauran ayyukan tituna da ake yi a cikin babban birnin Abuja baki ɗaya ba.

Wike ya yi alƙawarin kammala manyan tituna

Wike ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa za a kammala wasu manyan ayyukan tituna guda biyu kafin ƙarshen shekarar nan.

"Ina tabbatar wa shugaban ƙasa cewa titin daga Apo zuwa Karshi za a kammala shi kafin ƙarshen wannan shekara. Haka kuma titin daga Bwari zuwa Kubwa za a kammala shi kafin ƙarshen shekarar."

A cewarsa, ayyukan titunan da ake yi sun kawo sauyi a ƙauyukan da ke wajen tsakiyar birnin Abuja, tare da nuna cewa gwamnatin Tinubu na kai ayyukan ci gaba zuwa yankunan da aka daɗe ana watsi da su.

Wike ya ce zai yi murabus daga mukaminsa
Wike a jawabi a wajen taron jam'iyyar PDP Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Wike ya yi alƙawarin yin murabus

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce duk bayanan da ya gabatar ana iya tantance su, saboda haka ya ƙalubalanci masu sukarsa su fito su tabbatar da akasin abin da ya faɗa.

Kara karanta wannan

Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu

"Idan akwai wani da ke da ra'ayi na daban, ya fito ya nuna cewa abin da muke faɗa ba daidai ba ne. Zan yi murabus daga mukamina na Ministan Babban Birnin Tarayya."

- Nyesom Wike

Wike ya magantu kan PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yi wahala jam'iyyar PDP ta sake lashe zaben shugaban kasa a 2027 a halin da take ciki.

Wike ya bayyana cewa babu ta yadda PDP za ta iya lashe zabe matukar ba ta fara gyara tsarinta na cikin gida da warware rikice-rikicen da ke addabarta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com