Bayan Malami, Kotu Ta Bayar da Umarnin Kwace Kadarorin N8.94bn a hannun 'Yar Kasuwa
- Babbar kotun babbar birnin tarayya Abuja da ke Apo ta ba da umarnin kwace kadarorin shahararriyar 'yar kasuwa, Aisha Achimugu
- Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta samu nasara bayan gabatar da bukatar kwace kadarorin a gaban kotu
- Kadarorin da kotu ta umarci a kwace sun haɗa da kayan ado, motoci 11 na alfarma, dalar Amurka $50,000 da kuma Naira miliyan 30
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun babban birnin tarayya Abuja da ke Apo ta ba da umarnin kwace kadarorin da ake alaƙanta wa da fitacciyar 'yar kasuwa, Aisha Achimugu.
Kotun ta bayar da umarnin kwace kadarorin ne na 'yar kasuwar kuma wacce ta kafa kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Ltd.

Source: Facebook
An umarci kwace kadarorin Achimugu
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa Mai shari'a Jude Onwugbuzie ne ya ba da umarnin kwace kadarorin har abada ga gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne bayan amincewa da bukatar da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta gabatar, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
Kadarorin da kotun ta ba da umarnin a kwace sun haɗa da kayan ado masu darajar Naira biliyan 4.645, motoci 11 na alfarma da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.293, dalar Amurka $50,000 da kuma tsabar kudi Naira miliyan 30.
Yadda lamarin Aisha Achimugu ya fara
A watan Janairun 2024, Aisha Achimugu ta ja hankalin jama'a bayan ta shirya bikin cika shekaru 50 da haihuwa na tsawon kwana bakwai a tsibirin Grenada da ke yankin Caribbean.
Manyan fitattun mutane daga masana'antar nishaɗi ta Najeriya da sauran jiga-jigan ƙasa sun halarci bikin.
Bayan fiye da shekara guda, EFCC ta ayyana Achimugu a matsayin wacce ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a safarar kuɗaɗen haram.
A ranar 29 ga Afrilu, 2025, jami'an EFCC sun kama ta a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
EFCC ta kwace wasu kuɗaɗe

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: Kotu ta kwace kadarori 48 na Malami a Abuja, Kano da wasu jihohi
A watan Maris na 2026, Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace dalar Amurka miliyan 13 da ake zargin suna da alaƙa da Aisha Achimugu da kuma kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Ltd.
Mai shari'a Emeka Nwite ya ce EFCC ta gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu cewa kuɗaɗen sun samo asali ne daga ayyukan damfara.

Source: Facebook
Bayan hukuncin, kamfanin ya bayyana cewa ya fara shirin ɗaukaka ƙara domin kalubalantar umarnin kwace kadarorin.
A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kuɗaɗen da ake zargin suna da alaƙa da kamfanin Achimugu, an kuma samu rahotannin da ke zargin cewa wasu 'yan siyasa ne ke mara mata baya.
Kotu ta umarci kwace kadarorin Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarorin tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.
Kotun ta bayar da umarnin kwace kadarorin guda 48 wadanda ke a jihohin Kebbi, Kano Abuja da Kaduna bayan EFCC ta bukaci hakan.
Asali: Legit.ng
