Emefiele: Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe kan Kwace Kadarorin Tsohon Gwamnan CBN
- Kotun Kolin Koli ta tabbatar da hukuncin kwace kadarori bakwai, dala miliyan 2.045 da takardun hannun jari da ake alakanta wa Godwin Emefiele
- Kotun ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da mayar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a Legas
- EFCC ta ce bincike ya nuna ana kyautata zaton kadarorin an mallake su ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Kotun Kolin Koli ta Najeriya a ranar Juma'a, 17 ga Yuli, 2026, ta tabbatar da hukuncin ƙarshe na kwace da ke da alaka da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Kotun ta tabbatar da kwace filaye bakwai $2,045,000 da kuma takardun hannun jari da ake alakanta wa da Godwin Emefiele, tare da mayar da su mallakin gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Hukumar EFCC ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X a ranar Juma'a, 17 ga watan Yulin 2026.
Kotun ta yanke hukunci na bai daya ta hannun kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ibrahim Mohammed Saulawa.
Kotun ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke, sannan ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, wadda ta umarci a kwace kadarorin bisa zargin cewa an mallake su ne da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar ayyukan da ba su dace da doka ba.
Yadda shari'ar ta kai Kotun Koli
Bayan Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin kwace kadarorin, Godwin Emefiele ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadda ta soke hukuncin kotun farko.
Sai dai Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), wadda ba ta gamsu da hukuncin ba, ta garzaya Kotun Kolin Koli domin neman a sake duba lamarin.
A hukuncin da ta yanke yanzu, Kotun Kolin Koli ta mayar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya tare da tabbatar da shi baki ɗaya.
Kadarorin da aka kwace
Kadarorin da kotu ta tabbatar da kwace su sun haɗa da:
- Katafaren gida mai zaman kansa da ke lamba 17B, titin Hakeem Odumosu, Lekki Phase 1, Legas
- Filinda ba a gina ba mai faɗin murabba'in mita 1,919.592 a Oyinkan Abayomi Drive (tsohon Queens Drive), Ikoyi, Legas
- Gidan bene ɗaya da ke lamba 65A Oyinkan Abayomi Drive, Ikoyi, Legas
- Gidan duplex mai ɗakuna huɗu da ke 12A Probyn Road, Ikoyi, Legas
- Ginin masana'antu da ake yi a kan filaye 22 a Agbor, jihar Delta
- Rukunin gidaje takwas da ke kan fili mai faɗin murabba'in mita 2,457.60 a lamba 8A Adekunle Lawal Road, Ikoyi, Legas
- Wani cikakken gidan duplex tare da dukkan abubuwan da ke cikinsa a fili mai faɗin murabba'in mita 2,217.87 da ke 2A Bank Road, Ikoyi, Legas
Baya ga waɗannan kadarori, Kotun Kolin Koli ta kuma umarci a kwace $2,045,000 da kuma takardun hannun jarin kamfanin Queensdorf Global Fund Limited tare da mayar da su mallakin gwamnatin tarayya.

Source: Getty Images
Kotu ta kwace kadarorin Aisha Achimugu
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun babban birnin tarayya Abuja da ke Apo ta ba da umarnin kwace kadarorin da ake alaƙanta wa da fitacciyar 'yar kasuwa, Aisha Achimugu.
Kotun ta bayar da umarnin kwace kadarorin ne na 'yar kasuwar kuma wacce ta kafa kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Ltd.
Asali: Legit.ng


