Mary Habila: Sababbin Bayanai Sun Fito kan Mutuwar Budurwa a Gidan Ministan Tinubu
- Anita Baaki ta ce ita ce ta yi magana da Mary Habila na ƙarshe kafin rasuwarta a gidan Ministan ayyuka, David Umahi
- Ta bayyana cewa Mary Habila ta sanar mata da cewa za ta yi wanka kafin ta kwanta barci bayan sun gama hira da daddare
- Washegari dai an gano Mary Habila a sume a ɗakinta, daga baya likitoci suka tabbatar da rasuwarta bayan an kai ta asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sababbin bayanai sun fito kan yanayin mutuwar Mary Habila, wata ma'aikaciyar jinya da ke aiki a jami'ar DUFUS, wadda aka tura aiki zuwa Ma'aikatar Ayyuka ta Tarayya.
Abokiyar aikinta kuma ƙawarta ta kusa, Anita Baaki, ta bayyana cewa ta yi magana da Mary Habila da daddare..

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Anita Baaki ta bayyana abin da ya faru a cikin bayanan da ta gabatar a babbar kotun jihar Ebonyi.
Baaki, wadda ƙwararriya ce a fannin motsa jiki daga jihar Benue, ta ce tana cikin ma'aikatan da suka yi tafiya daga Abuja zuwa jihar Ebonyi ranar 24 ga Yunin 2026 domin gudanar da aiki ƙarƙashin Ministan Ayyuka, David Umahi.
Yadda aka sauka a masaukin ma'aikata
A cewar Baaki, an sauke ma'aikatan ne a ɗakuna daban-daban amma masu maƙwabtaka a wani bangare na ma'aikata da ke cikin harabar gidan David Umahi da ke Uburu, ƙaramar hukumar Ohaozara.
Ta jaddada cewa ginin an tanade shi ne domin ma'aikata da baƙi masu alaƙa da aiki, ba gidan zaman Ministan ba ne, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
Ganawa ta ƙarshe da Mary Habila
Baaki ta ce a yammacin ranar 26 ga Yunin 2026, Mary Habila ta dawo bayan ta gyara gashinta, sannan ta shigo ɗakinta domin nuna mata sabon salon gashin.
Ta ce sun yi hira tare da raha kafin Mary Habila ta bayyana cewa ta gaji kuma za ta yi wanka kafin ta kwanta.
"Mary ta gaya min cewa ta gaji kuma tana son yin wanka kafin ta yi barci. Wannan ne karo na ƙarshe da na gan ta da rai," in ji Baaki.
Yadda aka gano gawar Mary Habila
Baaki ta ce da safe washegari ta damu bayan Mary Habila ba ta fito kamar yadda ta saba ba. Ta ce duk kiran wayar da aka yi mata bai shiga ba, lamarin da ya sa ta je ta buga ƙofar ɗakinta.
Da ta ga ƙofar a kulle daga ciki kuma babu amsa, sai ta sanar da wani ma'aikacin gidan domin a bincika ko tana wani wuri a harabar.
Bayan an tabbatar ba a same ta a ko'ina ba, an sanar da sauran ma'aikata, inda daga bisani aka balle ƙofar ɗakin.
A cewarta, an tarar da Mary Habila kwance a sume a ƙasa kusa da ƙofar ɗakin, inda nan take aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya ta David Umahi, inda likitoci suka tabbatar da cewa ta rasu kafin isowarta.

Source: Facebook
Ba a tursasa mata yin bayani ba
Anita Baaki ta bayyana cewa ta bayar da bayanan ne da son ranta ba tare da wani matsin lamba ko tilastawa ba.
Ta ce manufar shaidar ita ce ta taimaka wa hukumomi wajen gudanar da binciken da ake yi kan lamarin.
An bukaci Umahi ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa ADC ta kara matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan mutuwar Mary Habila A gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, da ke Ebonyi.
Jam'iyyar ta bukaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano hakikanin abin da ya faru da marigayiyar a gidan ministan ba tare da tasirin gwamnati ba.
Hakazalika, ADC ta bukaci David Umahi ya ajiye mukaminsa na wucin gadi domin bai wa binciken cikakken 'yanci da kuma karfafa amincewar jama'a.
Asali: Legit.ng


