Tinubu Ya Sanya Hannu kan Wata Sabuwar Doka, Ta Shafi Harkokin Kudade a Intanet

Tinubu Ya Sanya Hannu kan Wata Sabuwar Doka, Ta Shafi Harkokin Kudade a Intanet

  • Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da za ta hada hukumomi wajen tsara dokokin kadarorin zamani da kuma dakile damfara a Najeriya
  • Sabuwar dokar ta kafa Majalisar Kula da Kadarorin Zamani karkashin bankin CBN domin hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da kare tsarin kudi
  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta samar da tsarin gwaji, manufofin haraji da takardar bayanai domin bunkasa fannin kadarorin zamani cikin tsaro da gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Zartarwa ta Shugaban Kasa kan Daidaita Tsarin Kula da Kadarorin Zamani ta 2026, domin inganta yadda ake tsara dokokin wannan bangare a Najeriya.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce dokar ta fara aiki nan take, kuma an kafa ta ne bisa ikon da sashe na 5 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da ta kafa majalisar kula da kadarorin zamani
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na sanya hannu kan wata takarda. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Gwamnati za ta dakile damfara da safarar kudade

Ma'aikatar yada labarai da wayar da kai ta tarayya ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a yau Juma'a, 17 ga watan Yulin 2026.

Gwamnati ta bayyana cewa dokar za ta taimaka wajen hada kan hukumomin da ke kula da harkokin kudi, kasuwannin hannayen jari da tattara kudaden shiga, tare da kare 'yan Najeriya daga damfara da sauran laifukan da ke da alaka da kadarorin zamani, in ji rahoton

A cewar gwamnatin tarayya, bunkasar amfani da kadarorin zamani ta haifar da rudani saboda wasu hukumomi na aiki ba tare da cikakken hadin kai ba.

Ta ce hakan ya bar gibi da masu damfara, masu safarar kudade, masu daukar nauyin ta'addanci da masu aikata laifukan intanet suka rika anfani da su wajen cutar da jama'a.

Sanarwar ta ce sabuwar dokar ba ta kafa wata sabuwar hukuma ba, amma za ta tabbatar da cewa hukumomin da ke da alhakin kula da bangaren suna aiki tare domin rufe gibin da ke akwai.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta gabatar da ƙudurin da zai jawo babbar matsala ga Najeriya

An kafa majalisar da CBN zai jagoranta

Dokar ta kafa Majalisar Kula da Kadarorin Zamani, wadda Babban Bankin Najeriya (CBN) zai jagoranta.

Hukumar Haraji ta Kasa (NRS) da Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari (SEC) za su kasance mataimakan shugabannin majalisar, yayin da Hukumar Binciken Harkokin Kudade (NFIU) da Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) za su kasance mambobi.

Majalisar za ta tsara manufofi, ta karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi, tare da aiki da Babban Lauyan Tarayya wajen samar da tsarin doka da zai dace da bukatun tsaro da tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa majalisar kula da harkokin kadarorin intanet
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da zai jagoranci taron majalisar FEC. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Za a kafa ofishin gudanarwa da tsarin gwaji

Dokar ta kuma kafa Ofishin Kula da Kadarorin Zamani, wanda zai kasance karkashin CBN domin gudanar da ayyukan yau da kullum da musayar bayanai tsakanin hukumomin gwamnati.

Hakazalika, CBN zai bude wani tsarin gwaji, inda kamfanonin da suka cancanta za su rika gwada sababbin kayayyaki da ayyukan da suka shafi fasahar blockchain da kadarorin zamani karkashin kulawa ta musamman.

Kara karanta wannan

Hotunan jami'a, gidan rediyo da sauran kadarori 46 da aka kwace a hannun Malami

Gwamnati ta ce wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa duk wata sabuwar fasaha da za ta shiga kasuwar Najeriya ta cika ka'idojin kare masu amfani da kuma tabbatar da zaman lafiyar tsarin kudi.

Tinubu ya yi watsi da kudurori 2

A wani labari, mun ruwaito cewa, Bola Ahmed Tinubu bai gamsu da wasu kudirori da Majalisar tarayya ta aika masa ana neman sa hannunsa ba.

Shugaban kasa ya rubuta wasika zuwa ga Godswill Akpabio dauke da kura-kuran da aka yi wajen aikin kudirorin.

Idan an sake yin kwaskwarima, shugaba Tinubu ya fada wa majalisa a shirye yake ya amince kudirorin su zama dokoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com