Mary Habila: Dalilin da Ya Sa Iyayen Budurwar da Ta Mutu a Gidan Minista Ba Su So a Binciki Gawarta
- Shugabar karamar hukumar Jaba, Larai Ishaku, ta ce marigayiya Mary Habila ƙwararriyar ma'aikaciyar lafiya ce mai jajircewa
- Ta bayyana cewa Mary tana cikin tawagar likitocin da ke kula da lafiyar Ministan Ayyuka, David Umahi
- Shugabar ta kuma ce mahaifin marigayiyar ya ƙi a yi mata gwajin gano musabbabin mutuwa saboda ya yi imanin hakan ba zai dawo da rayuwarta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jaba, Kaduna – Shugabar ƙaramar hukumar Jaba ta jihar Kaduna, Larai Ishaku, ta yi magana kan mutuwar ma'aikaciyar jinya, Mary Habila, a gidan David Umahi.
Larai Ishaku ta bayyana marigayiya Mary Habila a matsayin ƙwararriyar ma'aikaciyar lafiya mai jajircewa da ta sadaukar da aikinta wajen tallafa wa bukatun lafiyar Ministan Ayyuka, David Umahi.

Source: Getty Images
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa ta bayyana hakan ne yayin da take ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiyar.
Larai Ishaku ta ce Mary tana cikin tawagar ma'aikatan lafiya da aka ɗora wa alhakin kula da lafiyar David Umahi, inda ta yi aiki tare da sauran abokan aikinta domin tabbatar da cewa ana kula da lafiyarsa yadda ya kamata.
Meyasa iyayenta suka ƙi gwajin gawa?
Shugabar ƙaramar hukumar ta kuma bayyana dalilin da ya sa iyayen Mary Habila suka ƙi amincewa a yi mata gwajin gano musabbabin mutuwa.
"A cewar Baba Habila, ya yanke shawarar kada a yi gwajin gawa ne bisa ra'ayinsa cewa babu wani binciken likitanci da zai iya dawo da ran 'yarsa."
"Ya kuma bayyana cewa ba ya da wata ƙiyayya ko ƙorafi a kan Ministan ayyuka ko iyalansa. Ya ce yana da yaƙinin cewa 'yarsa ta rayu cikin mutunci da gaskiya, kuma ba ta taɓa ba shi abin damuwa ba."
- Larai Ishaku
Ta ƙara da cewa Baba Habila ya roƙi jama'a su bari 'yarsa ta huta lafiya, tare da guje wa yaɗa jita-jita ko hasashe marasa tushe game da yadda ta rasu.
Har ila yau, ta ce mahaifin marigayiyar ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar Ebonyi da su taimaka wajen sakin gawar 'yarsa domin iyalanta su yi mata jana'iza cikin mutunci daidai da al'adunsu da bukatunsu.

Kara karanta wannan
Umahi: A karshe ministan Tinubu da aka tsinci gawar budurwa a gidansa ya fadi abin da ya faru
An yaba da sadaukarwarta
Larai Ishaku ta bayyana matuƙar alhini kan rasuwar Mary Habila, tana mai cewa ƙwararriyar ma'aikaciyar lafiya ce mai ƙwazo wadda gudummawar da ta bayar za ta ci gaba da kasancewa cikin tunanin waɗanda suka yi aiki tare da ita.
Ta kuma miƙa ta'aziyyarta ga iyalan Habila, tare da addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi, Ya kuma jikanta da rahama.

Source: Twitter
Yadda aka ce aka gano gawarta
Mary Habila tana cikin tawagar ma'aikatan lafiya da suka raka Ministan Ayyuka, David Umahi, zuwa garinsu na Uburu da ke ƙaramar hukumar Ohaozara a jihar Ebonyi.
Rahoton The Punch ya ce an tsinci gawarta ne a cikin harabar gidan Ministan, yayin da ake zargin ta rasu a can. Har yanzu ba a bayyana a hukumance musabbabin mutuwarta ba.
Maganar Umahi kan mutuwar Mary Habila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi magana kan mutuwar hadimarsa, Mary Habila, wadda ta rasu a gidansa..
Umahi ya ce ba ya zargin an aikata wani laifi kan marigayiyar, yana mai cewa kokarin alakanta shi da lamarin siyasa ce da ta wuce gona da iri.
Asali: Legit.ng
