Babban Jigo a Haɗakar Su Atiku Ya Fice daga ADC, Ya Ɗora Laifin kan El Rufai
- Salihu Lukman ya fice daga jam'iyyar ADC da kawancen 'yan adawa, yana mai dora laifin hakan a kan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai
- Lukman ya ce an ware shi daga yanke hukunci kan shugabancin kawancen 'yan adawa a Kaduna duk da rawar da ya taka wajen hada kan tafiyar
- Tsohon jigon APC ya ce ya rasa kwarin gwiwa kan makomar kawancen, yana zargin wasu shugabanni da maimaita salon siyasar da suke suka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ADC da kuma kawancen jam'iyyun adawa.
Salisu Lukman ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aikewa shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, tare da kwafen wasikar ga shugabannin kawancen.

Source: Facebook
Lukman ya fice daga ADC saboda 'El-Rufai'
Kusan 'yan adawar ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda abin da ya kira ci gaba da fuskantar adawa da cin zarafi daga tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da wasu magoya bayansa, in ji rahoton Daily Trust.
A cewarsa, an yi amfani da tsarin yanke hukunci kan shugabancin kawancen a Kaduna wajen ware shi, duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen gina hadin kan 'yan adawan.
Ya ce ya shafe fiye da shekara guda yana kokarin sasanta shugabannin adawa a Kaduna, amma daga bisani aka mayar da shi tamkar ba ya da wata kima a cikin kawancen.
Lukman ya rasa kwarin gwiwa kan ADC
Tsohon jigon APC ya ce ya fi dacewa ya dakatar da harkokin siyasarsa a cikin ADC da kawancen 'yan adawar fiye da ci gaba da fuskantar abin da ya bayyana a matsayin "kora da hali".
Jaridar The Guardian ta ruwaito Salihu Lukman ya kuma zargi wasu shugabannin kawancen da maimaita irin salon siyasar da suka dade suna sukar wasu da shi.
Lukman ya kuma yi ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, na tattaunawa da wasu mutane a Kaduna wadanda, a cewarsa, ba su da cikakken kudurin gina ADC, yayin da ake watsi da wadanda suka yi aiki wajen karfafa jam'iyyar.

Source: Facebook
Ya gode wa shugabannin kasa na kawancen
Duk da matakin da ya dauka, Salihu Lukman ya yaba wa shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, da sauran shugabannin kawancen a matakin tarayya.
Ya jaddada cewa matakin da ya dauka ba zanga-zanga ba ce kan shugabancin jam'iyyar na kasa, sai dai martani ne ga yadda, a cewarsa, El-Rufai da wasu shugabannin kawancen a Kaduna suka rika mu'amala da shi.
Lukman ya dade yana gargadin ADC
Idan ba a manta ba, a wani rahoton Legit Hausa na baya, kun ji cewa Salihu Lukman ya gargaɗi ADC kan yunƙurin wasu ƴan siyasa na mamaye komai a jam'iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban APC ya ce wasu daga cikin shugabannin haɗaka sun fara ƙoƙarin sanya mutanensu a shugabancin ADC da karfi da yaji.
Salihu Lukman ya ce hakan na nuna nan gaba, sai wanda suke so za a ba tikitin takara a kowane mataki a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng

