Manyan Labarai A Yau
Jigon APC ya zargi 'yan adawa da amfani da wata shari'a karkashin dokar neman bayanai ta Amurka (FOIA) da ta shafi Shugaba Bola Tinubu wajen neman biyan bukatu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya taya Gwamnan Zamfara Dauda Lawal murnar cika shekaru 61, yana yaba masa kan sauye-sauyen da ya kawo a jihar.
Gwamnatin Sokoto ta ayyana yaƙi da ’yan ta’adda tare da bai wa iyalan waɗanda aka kashe da waɗanda suka jikkata N9m bayan harin karamar hukumar Kebbe
Ɗan takarar SDP, Adewole Adebayo, ya zargi wasu jami’an gwamnati da haɗa kai da ’yan bindiga, yana mai cewa hakan na ƙara tsawaita matsalar tsaro.
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta ce sauya sheƙar ’yan siyasa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano ba za ta rage mata damar lashe zaɓen shekarar 2027 ba.
Dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur, gas da Jet A1 zuwa N200 kan lita idan ya lashe zaɓen 2027.
NELFUND ta musanta wani hoto da ke cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ɗaure ɗaliban da suka kasa biyan bashin karatu bayan kammala karatu.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda na Zamfara mai kula da ayyuka, DCP Asbagu Aliyu Muhammad, ya yi bankwana da duniya bayan fama da jinyar rashin lafiya.
Tsohon kwamishinan hukumar INEC, Festus Okoye, ya yi gargaɗin cewa sayen ƙuri’u da rashin tsaro na iya yin tasiri sosai kan zaɓen Najeriya na 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari