Pantami na Shirin 2027, Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 23 a Gombe
- Gwamna Inuwa Yahaya ya rantsar da sababbin kwamishinoni 23 tare da shugaban ma'aikata, masu ba shi shawara da sakataren dindindin a Gombe
- Gwamnan ya gargadi sabbin jami'an da su fara aiki nan take, yana mai cewa babu lokacin koyon aiki da saura ƙasa da shekara guda
- Inuwa Yahaya ya yi gargaɗi kan cin hanci da rashawa, tare da bayyana mukamin gwamnati a matsayin amanar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 23 tare da sabon shugaban ma'aikata, masu ba shi shawara na musamman da kuma sabon babban sakatare.
Gwamna ya taya kwamishinoni da hadiman murnar samun mukaman, yayin da yake jawabi a wajen bikin rantsarwar da aka gudanar a cibiyar taruka ta International Conference Centre da ke Gombe a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2

Source: Twitter
Gwamna ya rantsar da kwamishinoni
A taron, gwamnan ya tunatar da dukkan wadanda suka samu mukamin cewa sun ɗauki nauyin yi wa al'ummar jihar hidima cikin gaskiya, ƙwazo da riƙon amana, in ji rahoton Daily Trust.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an zaɓi sabbin jami'an ne daga ƙananan hukumomi 11 na jihar bisa ƙwarewa da cancanta.
Ya jaddada cewa kasancewar gwamnatin sa na daf da kammala wa'adinta, babu wani lokaci da za a ɓata wajen koyon yadda ake gudanar da aiki.
A cewarsa, jama'ar Gombe na da manyan buri daga gwamnati, saboda haka ya umarci sabbin kwamishinonin da su fara aiwatar da manufofin gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya kuma bukaci masu ba shi shawara na musamman su gabatar da sabbin dabaru da shawarwari da za su taimaka wajen hanzarta ayyukan ci gaban gwamnati.
Gwamnan ya yi gargaɗi kan cin hanci
Jaridar Tribune ta rahoto cewa Inuwa Yahaya ya gargadi sabbin jami'an da su guji cin hanci da rashawa, amfani da mukami ba daidai ba da kuma rashin ɗa'a.
Ya bayyana cewa mukamin gwamnati amana ce da ya kamata a yi amfani da ita domin bauta wa jama'a kaɗai.
A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai bata sunan gwamnatin jihar ba.
Gwamnan ya kuma bukaci sarakunan gargajiya, shugabannin al'umma da ƙungiyoyin farar hula su ba sabbin jami'an haɗin kai domin cika manufofin gwamnati.

Source: Original
Sunayen sababbin kwamishinoni
Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa da Abdulkadir Mohammed Waziri (Ma'aikatar Noma da Tsaron Abinci), Micah Sunday Hamman (Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki), Farfesa Aishatu Umaru Maigari (Ilimi), Sanusi Ahmad Pindiga (Makamashi da Albarkatun Ma'adinai), Yusuf K. Jalingo (Muhalli da Albarkatun Dazuzzuka), Muhammad Gambo Magaji (Kuɗi da Tattalin Arziki), da Farfesa Danladi Adamu Bojude (Lafiya).
Sauran sun haɗa da Mohammed Saidu Mohammed (Gidaje da Raya Birane), Aishatu Mohammed Bose Ahmed (Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci), Moses Kyari Bolda (Yaɗa Labarai da Al'adu), Adamu Dishi Kupto (Tsaron Cikin Gida), Barrister Zubairu Muhammad Umar (Shari'a), Ibrahim Shehu Turaki (Filaye), Salihu Baba Alkali (Bunkasa Kiwo), Barrister Sani Ahmad Haruna (Ƙananan Hukumomi), Lawanin Dankuka Faruk (Raya Karkara), Dr. Habu Dahiru (Kimiyya da Fasaha), Shehu Yerima Abdullahi (Ayyuka na Musamman), Nasiru Mohammed Aliyu (Kasuwanci da Yawon Buɗe Ido), Injiniya Bala Adams (Albarkatun Ruwa), Dr. Bertha Danja (Harkokin Mata), Dr. Usman Maijama'a Kallamu (Ayyuka da Gine-gine) da Yusuf Abdu Kwadon (Matasa da Wasanni).

Kara karanta wannan
Gwamna ya zakulo samari da zawarawa 300, zai masu auren gata da sadakin N250000 a Kebbi
Pantami ya shirya wa zaben Gombe
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya zargi masu rike da madafun iko a yau da handame dukiyar al’ummar da aka ba su amana.
Fitaccen malamin Musuluncin da yake neman zama gwamnan jihar Gombe ya gargadi masu mulki cewa murde zabe ba zai yiwu ba.
‘Dan takaran PDP a zaben 2027 ya ba ‘yan APC shawara su nemi yafiyar mutane saboda sun saba alkawuran da suka dauka.
Asali: Legit.ng
