Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanar da rasuwar tsohon ministan kimiyya da fasahar Najeriya, Farfesa Turner Isoun
- Marigayi Isoun ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa NITDA, da kuma kaddamar da tauraron dan adam na farko da Najeriya ta mallaka
- Gwamnan ya yabawa marigayin saboda gudummawarsa a ilimi, fasaha, da kokarinsa wajen samar da Bayelsa daga tsohuwar jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Farfesa Turner Isoun, wanda ya rasu yana da shekaru 87.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Daniel Alabrah, ya fitar ranar Juma'a a Yenagoa.

Source: Twitter
Najeriya ta yi rashin babban masani
Marigayi Isoun, wanda ya taba rike mukamin ministan kimiyya da fasaha tsakanin shekarun 2000 zuwa 2007 a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya rasu a Abuja ranar 15 ga watan Yuli, in ji rahoton Premium Times.
Gwamna Diri ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen masani a fannin likitancin dabbobi, wanda gudummawarsa ga ilimi da ci gaban kasa ba za a manta da ita ba.
Ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga al'ummar Ijaw, jihar Bayelsa da kuma Najeriya baki daya.
A cewarsa, marigayin ya kasance mutum mai gaskiya, hikima da kuma jajircewa wajen kare al'adun Ijaw da ci gaban al'ummarsa.
Tsohon ministan ya kafa tubalin jami'a
Gwamnan ya tuna cewa Isoun shi ne mataimakin shugaban jami'a na farko a tsohuwar jami'ar kimiyya da fasaha da ke Fatakwal, wadda yanzu ake kira jami'ar jihar Rivers.
Ya ce marigayin ya kafa tubali mai karfi ga jami'ar farko ta kimiyya da fasaha a Najeriya, sannan ya jagoranci sauye-sauye masu muhimmanci a fannin fasahar sadarwa lokacin da yake minista.
A karkashin jagorancinsa ne aka kafa Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), tare da Galaxy Backbone Plc domin inganta hanyoyin sadarwar gwamnati da fadada hanyoyin intanet a kasar.
Rawarsa a ci gaban sararin samaniya
Sanarwar ta kuma ce a lokacin da Isoun yake minista, Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin fasahar sararin samaniya.
A karkashin jagorancinsa aka kaddamar da tauraron dan adam na farko na Najeriya, NigeriaSat-1, da kuma NigComSat-1R, wadanda suka taimaka wajen bunkasa sadarwa da binciken kimiyya.

Source: Facebook
Baya ga haka, ya taba zama shugaban majalisar kungiyar Ijaw ta kasa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar samar da jihar Bayelsa daga tsohuwar jihar Rivers a shekarar 1996.
Gwamna Diri ya mika ta'aziyyar gwamnatin Bayelsa ga iyalan marigayin da al'ummarsa, yana mai kira gare su da su jajanta wa kansu da irin dimbin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya.
Asali: Legit.ng

