Mbappe Ya Zarce Messi, Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya

Mbappe Ya Zarce Messi, Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya

  • Kylian Mbappe na kasar Faransa ya zama dan wasan da ya fi kowa yawan zura kwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya
  • Dan wasan ya ci kwallaye biyu a wasan da Faransa ta sha kashi 6-4 a hannun Ingila a wasan neman lambar tagulla na Kofin Duniya na 2026
  • Kylian Mbappe ya kai kwallaye 22 a gasar cin Kofin Duniya, inda ya shiga gaban Lionel Messi da kwallo daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Kylian Mbappe ya zama dan wasan da ya fi kowa yawan zura kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya.

Kylian Mbappe ya samu wannan nasara ne bayan ya ci kwallaye biyu a wasan da Faransa ta sha kashi 6-4 a hannun Ingila a wasan neman lambar tagulla na gasar ta 2026.

Mbappe ya kere Messi
Lionel Messi da Kylian Mbappe na murnar zura kwallo a wasan Faransa da Ingila Hoto: Jamie Squire and Stefan Koops/EYE4IMAGES/NurPhoto.
Source: Getty Images

Kwallayen biyu sun kai adadin kwallayen da kyaftin din Faransa ya ci a tarihin gasar zuwa 22, inda ya wuce Lionel Messi da kwallo daya, cewar rahoton Yahoo Sports.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi kukan kura sun kama dan bindiga a jihar Kano

Lionel Messi zai fafata a wasan karshe da Argentina za ta yi da Spain ranar Lahadi, 19 ga watan Yulin 2026.

Mbappe ya zura kwallaye

Faransa ta yi wani gagarumin kokari a rabin lokaci na biyu domin kauce wa mummunan sakamako bayan Ingila ta riga ta ci ta 4-0 a rabin lokaci na farko.

Mbappe ya ci kwallon farko ta Faransa a minti na 48 bayan ya kammala wani kyakkyawan hari a cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Daga bisani ya ci kwallon Faransa ta uku a minti na 66, bayan Bradley Barcola ya zura kwallon ta biyu ga tawagar mintuna 12 da suka gabata.

Michael Olise ne ya ba abokin wasansa kwallo a bakin akwatin, inda kyaftin din Faransa ya buga ta cikin raga, wato kwallarsa ta 10 ga gasar.

Wannan kwallo ta kai adadin kwallayen Mbappe a gasar Kofin Duniya ta 2026 zuwa 10, inda ya ke gaban Messi da kwallaye biyu a matsayi na biyu.

Mbappe Ya Kafa Tarihi

TheCable ta ce Mbappe ya kuma zama dan wasan farko da ya ci akalla kwallaye 10 a gasar Kofin Duniya tun bayan da Gerd Muller na Jamus ya yi hakan a shekarar 1970.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Kyaftin din Faransa ya kara tazarar da ke tsakaninsa da sauran ‘yan wasa a tseren lashe kyautar takalmin zinare ta gasar, inda ya ke gaban wanda ke biye da shi da kwallaye biyu bayan ya kai 10.

Wannan nasarar tarihi ta kara tabbatar da matsayin Mbappe a cikin manyan ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye a tarihin gasar, tare da sanya shi cikin matsayi mafi karfi na kammala gasar Kofin Duniya na FIFA na 2026 a matsayin wanda ya fi kowa yawan kwallaye.

Mbappe ya zarce Messi
Kylian Mbappe na murnar zura kwalloa wasan Ingila da Lionel Messi a wasan Argentina Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

‘Yan wasan da suka fi kwallaye a gasar cin kofin duniya

  • Kylian Mbappe - kwallaye 22
  • Lionel Messi - kwallaye 21
  • Miroslav Klose - kwallaye 16
  • Ronaldo Nazario - kwallaye 15
  • Gerd Muller - kwallaye 14

Batun hoton Messi da Yamal

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar UNICEF ta tabbatar da sahihancin hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke nuna shahararrun 'yan wasan ƙwallon ƙafa, Messi da Yamal.

Tabbacin ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce da jita-jitar da aka yi ta yi na kwanaki cewa an sarrafa hotunan ne ta hanyar amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng