'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Kai Hari a Sokoto, an Kashe Jami'an Tsaro da Fararen Hula
- ’Yan kungiyar Lakurawa sun kai hari garin Girkau da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
- Harin ya yi sanadin mutuwar jami’in dan sanda da fararen hula biyu, yayin da wasu suka samu raunuka
- Maharan sun kona motocin jami’an tsaro biyu tare da yin awon gaba da shanu masu yawa yayin mummunan harin da suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Sokoto - Rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da wani hari da ’yan kungiyar Lakurawa suka kai garin Girkau da ke karamar hukumar Kebbe.
Harin da aka kai ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026 ya yi sanadiyyar mutuwar jami’in dan sanda da fararen hula biyu, yayin da wasu mutane suka samu raunuka.

Source: Original
’Yan sanda sun fatattaki maharan
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da jaridar The Punch ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026.
Maharan sun kuma kona motocin jami’an tsaro biyu mallakar rundunar ’yan sandan Najeriya da hukumar Sokoto State Community Guard Corps.
Ahmed Rufai ya ce rundunar ta samu kiran neman agaji, inda ta gaggauta tura jami’anta zuwa garin.
Ya ce jami’an tsaro sun yi musayar wuta da maharan, kuma daga bisani suka yi nasarar fatattakarsu.
Ahmed Rufai ya tabbatar da cewa jami’in dan sanda daya ya mutu yayin gudanar da aikinsa, yayin da aka lalata motocin jami’an tsaro biyu.
“Abin takaici, mun rasa daya daga cikin jami’anmu a harin. Mun samu kiran neman agaji daga al’ummar yankin, kuma nan take muka tura jami’anmu wurin.”
“Mun samu nasarar fatattakar ’yan bindigan Lakurawa, amma yayin musayar wuta, daya daga cikin jami’anmu ya rasa ransa.”
- Ahmed Rufai
Ya ce maharan sun kona motoci biyu, daya mallakar rundunar ’yan sanda, dayan kuma mallakar rundunar Sokoto State Community Guard Corps.
An kara tsaurara matakan tsaro
Ahmed Rufai ya ce rundunar ta kara kaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro a yankin. Ya kuma jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Mazauna yankin sun ce maharan dauke da makamai masu yawa sun afka garin tare da bude wuta kan jami’an tsaro da mazauna yankin. Hakan ya sa mutane da dama suka tsere domin neman mafaka.
Sunayen wadanda suka mutu
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka mutu akwai wani jami’in dan sanda mai suna Hussaini Manyu. Sauran sun hada da wani dattijo mai suna Bala Wakili da wani matashin makiyayi.
An ce an harbe matashin makiyayin ne har lahira bayan ya ki mika shanunsa ga maharan. Majiyoyin al’umma sun kuma bayyana cewa wani manomi ya samu raunukan harbin bindiga yayin da yake aiki a gonarsa.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kona mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka mutane 12 ciki har da wadanda suka kona a jihar Sokoto.
Hatsabiban 'yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Lajinge da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng

