Tirkashi: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Sake Yunkurin Sace Dalibai a Makaranta
- Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile yunƙurin sace ɗalibai da ake zargin ƴan ta’addan ISWAP ne suka kai makarantar FGGC Monguno
- 'Yan ta'addan na ISWAP sun farmaki makarantar amma sun fuskanci turjiya daga wajen hazikan dakarun sojoji
- Wasu ɗalibai sun mutu bayan harsasai daga ƴan ta’addan sun same su yayin musayar wuta tsakaninsu da dakarun sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun dakile yunƙurin sace ɗalibai da dama da ake zargin ƴan ta’addan ISWAP ne suka kai a jihar Borno.
'Yan ta'addan sun kai harin ne a makarantar Federal Government Girls College (FGGC), Monguno, da sanyin safiyar Lahadi, inda suka ceto ɗalibai 46.

Source: Original
Mukaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafin X a ranar Lahadi, 19 ga watan Yulin 2026.
'Yan ISWAP sun shiga makaranta a Borno
Kakakin ya ce lamarin ya faru ne bayan ƴan ta’addan sun samu damar shiga makarantar da taimakon wasu da ake zargin masu haɗin kai da su ne, da nufin sace ɗalibai da misalin ƙarfe 1:30 na dare ranar Lahadi.
Gwamnatin Borno na amfani da wurin ne a matsayin dakin kwanan dalibai na wucin gadi na daliban Federal Polytechnic Monguno.
Ya ce jami’an tsaro da ke cikin shiri sun hanzarta tunkarar ƴan ta’addan da ƙarfin wuta, lamarin da ya dakile shirinu, yayin da Sector 3 Quick Reaction Force (QRF) ta gaggauta ƙara ƙarfafa jami’an da ke makarantar.
“Da suka fuskanci ƙwarewar yaƙi da ƙarfin jami’an tsaro da kuma tsayin daka da suka nuna, ƴan ta’addan sun tilasta barin mugun shirin nasu tare da tserewa cikin rudani ba tare da sun cimma burinsu ba,” in ji shi.
An ceto ɗalibai 46
Kyaftin Goni ya ce wasu sassan gine-ginen makarantar sun lalace yayin arangamar, amma sojoji tare da jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun yi nasarar shawo kan lamarin.
“Bayan kammala aikin, sojoji sun yi nasarar ceto tare da kwashe ɗalibai 46 zuwa Kinnasara Barracks da ke Monguno, inda aka duba lafiyarsu nan take tare da ba su kulawar da ta dace,” in ji sanarwar.
Ya ce an tabbatar da cewa duk ɗaliban da aka ceto suna cikin kwanciyar hankali, kuma babu wani ɗalibi da aka sace.
Sai dai ya ce abin baƙin ciki shi ne, wasu ɗalibai sun mutu bayan harsasai da ƴan ta’addan suka harba suka same su yayin musayar wuta.
Ana farautar ƴan ta’adda
Operation HADIN KAI ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare rayukan mazauna yankin da kuma muhimman cibiyoyin gwamnati a Arewa maso Gabas, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Borno.
Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da kama mutanen da ake zargin sun taimaka wa ƴan ta’addan, yayin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke ci gaba da bin sawun ƴan ta’addan da suka tsere.

Source: Twitter
Ta ce Operation Hadin Kai za ta ci gaba da matsa lamba kan ƴan ta’adda ba tare da sassauci ba, tare da hana su samun damar gudanar da ayyukansu, lalata ƙarfin ayyukansu da kuma tabbatar da tsaron makarantu da sauran muhimman ababen more rayuwa a Arewa maso Gabas.
Sojoji sun cafke dan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da mayaƙan kungiyar ISWAP suka kai a Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Bayan fatattakar maharan, sun samu nasarar kama wani da ake zargin baƙon ɗan ISIS ne daga wata ƙasar Larabawa.
Asali: Legit.ng


