Babbar Magana: Abin da Trump Ya Ce bayan Iran ta Kashe Sojojin Amurka
- An kashe sojojin Amurka biyu a Jordan yayin da suke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sojojin da hare-haren Iran suka ritsa da su sun mutu ne “a bakin aiki domin kare ƙasarsu”
- Sojojin Amurka 16 sun mutu, yayin da sama da 430 suka jikkata tun bayan fara yaƙin a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana mutuwar sojojin Amurka biyu a Jordan a matsayin “abu mai matukar bakin ciki”.
Trump ya bayyana hakan ne bayan rundunar sojin Amurka ta yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar cewa an kashe su yayin da suke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran.

Source: Getty Images
Me Trump ya ce kan mutuwar sojojin?
A wata gajeriyar tattaunawa ta wayar tarho da jaridar NewsNation, Trump ya ce sojojin sun mutu ne “a bakin aiki domin kare ƙasarmu”.
Shugaban na Amurka ya sake jaddada cewa babban manufar yaƙin ita ce “kada a taɓa barin Iran ta mallaki makamin nukiliya”.
Da aka tambaye shi game da sanarwar Iran cewa ba za ta ƙara bin yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran ba, Trump ya ce: “Ban damu ko kaɗan ba.”
CENTCOM ta ce har yanzu ana neman wani soja na uku da ya ɓace, yayin da aka yi jinyar wasu sojoji huɗu da suka jikkata a harin sannan aka sallame su daga asibitocin Jordan.
Amurka ta ci gaba da kai hari
A ƙarshen ranar Asabar, CENTCOM ta kuma sanar da kammala wasu sababbin hare-haren sama da suka ɗauki sama da sa’o’i biyar a Iran.
Rundunar ta ce an kai hare-haren ne domin “gaggauta hukunta dakarun Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) da suka kai hare-hare kan sojojin Amurka a Jordan a daren jiya”.
Wannan shi ne karo na takwas a jere da Amurka ta kai hare-hare kan Tehran, bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wargaje saboda takaddamar iko kan mashigar ruwan Hormuz.

Source: Getty Images
Jami’ai sun sanar da cewa an kashe sojojin Amurka biyu a Jordan yayin da suke yaƙi da hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami na Iran.
Sojojin da suka jikkata an sallame su daga asibiti, yayin da sauran jami’an da aka duba saboda ƙananan raunuka suka koma bakin aiki.
CENTCOM ta ce ba za ta bayyana sunayen sojojin da aka kashe ba har sai an sanar da danginsu na kusa.
Tun bayan fara yaƙin, adadin sojojin Amurka da aka kashe ya kai 16, yayin da sama da 430 suka jikkata.
Iran ta jikkata sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kai hare-hare kan sansanin sojojin Amurka a kasar Jordan.
An kai hare-haren ne kan aƙalla sansanonin soji biyu da ke Jordan, inda aka tabbatar da jikkatar wasu jami'an sojin Amurka da dama.
Asali: Legit.ng

