Kasashen Africa da Za Su Iya Shiga Jamus a 2026 ba Tare da Takardar Biza ba
- Gwamnatin Jamus ta amince wa wasu kasashe biyu daga nahiyar Afirka su shiga ƙasar ba tare da neman biza ba domin gajeren zama
- Najeriya na cikin ƙasashen Afirka da har yanzu ake bukatar ’yan ƙasarsu su nemi bizar shiga Jamus kafin su yi tafiya zuwa ƙasar
- Masu fasfon Mauritius da Seychelles za su iya shiga Jamus ba tare da biza ba, amma dole su bi sharuddan zama da dokokin ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Jamus - Gwamnatin Tarayyar Jamus ta fitar da sabon bayani kan dokokin biza ga baƙi masu shirin shiga ƙasar.
Yayin da al'ummar mafi yawan ƙasashen Afirka, ciki har da Najeriya, ke bukatar samun bizar shiga kafin tafiya, akwai ƙasashe biyu kacal a nahiyar da aka ba ’yan ƙasarsu damar shiga Jamus ba tare da biza ba.

Source: UGC
Sababbin ƙa’idojin sun nuna cewa masu fasfo daga waɗannan ƙasashe biyu na iya shiga Jamus domin ɗan gajeren zama ba tare da bin tsauraran matakan neman bizar Schengen ba, cewar rahoton shafin gwamnatin Jamus.
Kasashen Afirka da ke shiga Jamus ba biza
A cewar bayanan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus ta wallafa, ƙasashen Afirka biyu da aka cire daga dokar neman bizar shiga Jamus su ne:
- Mauritius
- Seychelles
Waɗannan ƙasashen tsibiri biyu na daga cikin masu fasfo mafi ƙarfi a Afirka, wanda ke ba ’yan ƙasarsu damar shiga ƙasashe da dama cikin sauƙi, ciki har da ƙasashen yankin Schengen.
Sharuddan shiga ba tare da biza ba
A ƙarƙashin sabbin ƙa'idojin, masu fasfo daga Mauritius da Seychelles za su iya zama a Jamus na tsawon kwanaki 90 kacal cikin duk kwanaki 180. Bayan wannan wa'adi, dole ne su bar ƙasar ko kuma su nemi izinin zama idan ya dace.
Haka kuma, duk wanda ya shiga Jamus ta wannan tsarin ba a ba shi damar yin wani aiki da ake biyan kuɗi ba. Wannan yana nufin rangwamen ya shafi yawon buɗe ido, ziyara ko wasu dalilai na ɗan gajeren zama kawai.
Ga ’yan ƙasar Seychelles kuwa, gwamnatin Jamus ta bayyana cewa rangwamen ya shafi masu fasfo na zamani masu bayanan 'biometric' kawai. Duk wanda ke amfani da tsohon fasfo mara bayanan halitta dole ne ya nemi biza kafin tafiya.

Source: Twitter
Matsayin Najeriya
Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen da ke bukatar bizar shiga Jamus. Don haka duk ɗan Najeriya da ke son tafiya ƙasar dole ne ya cika sharuddan neman bizar Schengen tare da samun amincewa kafin tafiya.
Sai dai gwamnatin Jamus ta yi bayanin cewa idan ɗan Najeriya yana da fasfo na wata ƙasa da aka ba rangwamen shiga ba tare da biza ba, kamar Mauritius, Seychelles, Birtaniya, Amurka, Kanada ko wata ƙasar Tarayyar Turai, zai iya shiga Jamus ta amfani da wannan fasfo ba tare da neman biza ba, muddin ya cika sauran sharuddan shige da fice.
Bayani kan bizar shiga Jamus
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Jamus za ta ci gaba da bai wa 'yan kasashe 62 damar shiga ba tare da biza ba domin zama na kankanin lokaci a cikin kasar.
Matafiya za su iya zama har zuwa kwanaki 90 cikin kwanaki 180 domin yawon bude ido, ziyarar iyali ko harkokin kasuwanci ba biza.
Jamus ta fadi makomar Najeriya da karin wasu kasashen kan ko wasu daga cikin 'yan kasar za su ci gajiyar zama a cikinta ba tare da biza ba.
Asali: Legit.ng


