Gwamnatin Trump Ta Dauki Sabon Mataki da Zai Shafi Dalibai da 'Yan Jaridar Najeriya
- Amurka ta sanar da kawo ƙarshen tsarin zama ba tare da iyaka ba ga ɗalibai da 'yan jarida na ƙasashen waje
- Sabuwar dokar ta kayyade lokacin zama zuwa mafi yawan shekara huɗu, sai an nemi ƙarin izini idan akwai buƙata
- Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta ce matakin zai taimaka wajen dakile amfani da biza ta hanyar da ba ta dace ba da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta sanar da wata sabuwar doka da ta kawo ƙarshen tsarin da ke bai wa ɗaliban ƙasashen waje, baki da 'yan jarida damar zama a ƙasar ba tare da ƙayyadadden lokaci ba.
Ma'aikatar Tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, 16 ga watan Yulin 2026.

Source: Getty Images
Jaridar Washington Post ta kawo rahoton matakin da ma'aikatar ta dauka a ranar Alhamis, 17 ga watan Yulin 2026.
inda ta soke tsarin da ake kira "duration of status", wanda ke bai wa masu bizar F, J da I damar ci gaba da zama a Amurka muddin suna cika sharuɗɗan karatu ko shirinsu ba tare da ana sake tantance su akai-akai ba.
Dalilin sauya tsarin biza a Amurka
A cewar DHS, an ɗauki wannan mataki ne domin dawo da mutuncin tsarin shige da fice na Amurka, dakile amfani da biza ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar ci gaba da tantance masu zama a ƙasar.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa sabon tsarin ya daidaita manufar bizar ɗalibai da sauran nau'o'in bizar baƙi waɗanda tuni suke da ƙayyadadden lokacin zama.
Abin da minista ya ce
Ministan DHS, Markwayne Mullin, ya ce:
"Tsawon kusan rabin ƙarni, tsohon tsarin zama ba tare da iyaka ba ya raunana tsaron ƙasa tare da samar da damar yin zamba a harkar shige da fice."
"Tsawon shekaru da dama, ana barin ɗaliban ƙasashen waje su zauna a Amurka ba tare da iyaka ba, lamarin da ya bai wa dubban mutane damar ci gaba da yin rajistar karatu domin kauce wa barin ƙasar."
"Ta hanyar kafa ƙayyadaddun wa'adin waɗannan biza, Amurka na dawo da ikon tantancewa, bincike da sa ido kan mutanen da ke cikin iyakokinta yadda ya kamata."
Yadda sabuwar dokar za ta yi aiki
A ƙarƙashin sabuwar dokar, ɗaliban da ke da bizar F da kuma baki masu bizar J za su samu izinin zama ne kawai na tsawon lokacin shirin karatunsu, amma ba zai wuce shekara huɗu ba.
Idan ɗalibi na buƙatar ƙarin lokaci domin kammala karatunsa, dole ne ya nemi ƙarin izinin zama kai tsaye daga hukumar USCIS.
DHS ta ce duk wanda ya nemi ƙarin lokaci zai fuskanci ɗaukar bayanan halittu, binciken tarihin sa da kuma tantance yiwuwar zamba, inda za a mayar da ikon sa ido daga jami'o'i zuwa hukumomin gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Batun cafke Tinubu idan ya je Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa jakadan dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa.
Jimoh Ibrahim ya musanta rade-radin cewa Shugaba Bola Tinubu na fuskantar barazanar kama idan ya je Amurka.
Asali: Legit.ng

