Tura Ta Kai Bango: Mutanen Gari Sun Aika Sako ga Tinubu kan Hare Haren 'Yan Bindiga
- Mazauna Lata Nna a karamar hukumar Patigi ta Jihar Kwara sun roki Shugaba Bola Tinubu ya kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane
- Sun ce ba su iya zuwa gonaki da kasuwa, yayin da hanyar da ta hada su da sauran al’umma ta zama barazana ga rayuwarsu
- Al’ummar ta kuma bukaci a gudanar da samamen tsaro mai dorewa domin fatattakar ‘yan bindiga daga maboyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Mazauna al’ummar Lata Nna da ke karamar hukumar Patigi a jihar Kwara, sun mika kokensu ga Shugaba Bola Tinubu.
Mazauna garin sun roki Shugaba Bola Tinubu ya sa baki kan hare-haren ‘yan bindiga, sace mutane da sauran laifuffuka da suka addabi yankin tsawon shekaru biyu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar neman agaji (SOS) da aka aika wa shugaban kasar.
Sakataren kungiyar matasan Lata-Nna, Tauheed Desco, ya yi kira a madadin al’ummar yankin da a gaggauta tura taimakon gwamnatin tarayya, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Wani bangare na wasikar na cewa:
“Mai girma shugaban kasa, ba za mu iya zuwa gonakinmu ba, ba za mu iya zuwa kasuwa ba, kuma ba za mu iya kwanciya barci cikin kwanciyar hankali ba. Hanyarmu daya tilo ta zama hanyar mutuwa. Al’ummarmu na zubar da jini.”
Mazauna yankin sun roki shugaban kasa da ya bayar da umarnin gaggauta tura jami’an tsaro zuwa Lata Nna domin kare al’ummar tare da sake bude hanyar da ta hada su da sauran wurare.
Sun kuma bukaci a tallafa wa iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da su tare da tabbatar da adalci, musamman iyalan Alhassan Ndaba da wasu mazauna biyu da aka kashe a wani hari ranar 26 ga Yuni.
Hare-Haren sun addabi al’umma
Al’ummar ta ce ta shafe lokaci tana fama da sace mutane, karbar kudin fansa, kutsen ‘yan bindiga cikin gonaki da fashi da makami.
Sai dai ta ce wasu hare-haren da ta lissafa ne suka sa halin da take ciki ya fito fili saboda girman hare-haren, rashin tsoro da kuma muguntar da aka nuna.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya
Wasikar ta ci gaba da cewa:
“A watan Agustan 2025, an kashe mafarauta 65 a cikin daji yayin arangama tsakanin mafarautan da ‘yan bindiga, saboda karancin ingancin makaman da mafarautanmu ke amfani da su, yayin da ‘yan bindigar ke amfani da nagartattun makamai irin su AK-47 da makamantansu."
“An samu gawarwaki 40 kacal kuma aka binne su.”
An roki Shugaba Tinubu
A cikin wasikar neman agajin, mazauna yankin sun kuma roki shugaban kasa da ya bayar da umarnin gudanar da samamen tsaro mai dorewa domin fatattakar ‘yan bindiga daga maboyarsu da ke kewayen al’ummar.
Sun roki Tinubu da kada ya bari kungiyoyin masu aikata laifuffuka su mamaye Lata Nna, tare da yin kira gare shi da ya kawo musu dauki.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace masu rakiyar gawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun sace 'yan uwa uku da ke kai gawar mahaifiyarsu domin a yi mata jana'iza.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ohimini da ke jihar a Benue wanda ya tayar da hankalin al'ummomin yankin.
Asali: Legit.ng
